"Na Ɗauke Shi Uba," Tinubu Ya Kaɗu da Allah Ya Yi wa Jagoran Yarbawa Rasuwa
- Mai girma Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin mutuwar jagoran ƙungiyar al'adun yarbawa, PA Ayodele Adebanjo
- A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, Bola Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin dattijon kwarai mai kishin ƙasa
- Ya ce ya ɗauki Adebanjo a matsayin uba saboda gudummuwar da ya ba shi a siyasa musamman lokacin da yake neman zama gwamna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa matuka da rasuwar jigo a kungiyar yarbawa watau Afenifere, Pa Ayo Adebanjo.
Adebanjo ya rasu ne a ranar Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki a jihar Legas.

Asali: Facebook
Bola Tinubu ya yi ta'aziyar wannan rashi a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Bola Tinubu ya ɗauki marigayin uba
Tinubu ya bayyana Adebanjo a matsayin jagoran siyasa na kwarai, wanda ya kwashe tsawon shekaru yana fafutukar adalci, dimokuradiyya da dunkulewar kasa.
"Duk wanda ya san Baba Adebanjo ya shaida hikimarsa da kishin kasa da ke tattare da shi. An dade ana jin muryarsa a harkokin siyasa, kuma ba shakka, za a yi kewarsa," in ji Tinubu.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa duk da ana jimamin rashinsa, amma dole a godewa Allah da ya ba shi damar rayuwa mai albarka da cike da hidima ga kasa har tsawon shekaru 96.
Ya kara da cewa Adebanjo yana daga cikin shahararrun ‘yan gwagwarmaya na farko da suka taimaka wajen gina Najeriya.
A matsayinsa na lauya, dan siyasa, kuma mai fafutuka, ya kasance amitacce ga marigayi Cif Obafemi Awolowo, sannan ya taka rawar gani a jam'iyyun Action Group da Unity Party of Nigeria.
Tinubu ya faɗi gudummuwar da ya bayar
Haka nan, Tinubu ya jaddada cewa lokacin da aka soke zaben shugaban kasa na ranar 12 ga Yuni, 1993, Adebanjo ya tsaya tsayin daka wajen yakar mulkin soja.
A cewar shugaban ƙasa, marigayin yana daga cikin manyan muryoyin da suka taimaka wajen dawo da dimokuradiyya a Najeriya.
Shugaban kasa ya ƙara da cewa Adebanjo ya ba shi gudummuwa musamman lokacin da yake neman kujerar gwamnan Lagos a 1999.
"Ko da siyasarmu ta bambanta a baya-bayan nan, ba ta taba rage daraja da girmamawa da nake yi masa ba. Har zuwa rasuwarsa, ina kallonsa tamkar uba," in ji Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa ya miƙa sakon ta'aziyya
Daga karshe, ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayin, kungiyar Afenifere, gwamnonin Kudu maso Yamma, da duk ‘yan Najeriya da ke alfahari da irin hangen nesansa.
Shugaba Tinubu ya kammala da addu’a, yana mai fatan Allah ya gafarta wa Pa Ayo Adebanjo, ya sa ya huta.
Tinubu ya jajantawa Gwamna Makinde
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya aika saƙon ta'aziyya ga gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde bisa rasuwar yayansa.
Shugaba Tinubu, a cikin sakon ta’aziyyar, ya bayyana cewa rasa masoyi, musamman yaya da ake ƙauna, babban tashin hankali ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng