Kashim Shettima: "Arewa na Fama da Matsanancin Talauci"

Kashim Shettima: "Arewa na Fama da Matsanancin Talauci"

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Arewa maso Gabas na fama da matsanancin talauci duk da irin kokarin raya yankin
  • Shettima ya jinjina wa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC) kan saka jari a ilimi da fasahar koyo ta shirin ASSEP don inganta rayuwar matasa
  • Ya yi kira ga NEDC da sauran ma’aikatun gwamnati da su haɗa kai don tabbatar da inganta rayuwar mazauna shiyyar Arewa maso Gabas baki daya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana cewa yankin Arewa maso Gabas na fuskantar talauci mai tsanani.

Duk da haka, ya yaba wa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas (NEDC) kan saka hannun jari a fannin ilimi don fitar da yankin daga talauci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bayyana shirinta a kan ma'aikata a Najeriya

Kashim
Gwamnayin tarayya na son a kawo karshen talauci a Arewa maso gabas Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Leadership ta wallafa cewa Shettima ya ce tarihi ba zai manta da gudunmawar da hukumar ta NEDC ke bayar wa ba wajen farfado da yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ayyukan da hukumar NEDC ke yi ya wuce gyaran hanyoyin ababen more rayuwa zuwa zuba jari a ilimi da fasahar ilimi ta zamani ta hanyar shirin ASSEP.

Kashim Shettima ya gana da jami’an NEDC

Daily Post ta ruwaito cewa Sanata Shettima ya gana da shugabannin hukumar NEDC da suka ziyarce shi a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, don bashi rahoto kan ci gaban shirin ASSEP.

A jawabinsa, Shettima ya ce:

“Na yi matuƙar farin ciki da kokarin da NEDC ke yi, musamman Dr. Masha, wajen inganta shirin ASSEP. Abubuwa biyu da NEDC ta mayar da hankali a kai za sa ba za a manta su a tarihin kasar nan ba.
“Tabbas, gyaran ababen more rayuwa yana da kyau, amma wannan shirin ASSEP da kuma zuba jari a fasahar ilimi za su canza yanayin yankin gaba ɗaya.”

Kara karanta wannan

APC ta shawarci El-Rufa'i a kawo ƙarshen takun saka da gwamnatin Tinubu

Shettima ya yabi hukumar NEDC

Mataimakin shugaban kasar ya yaba wa tsarin da ASSEP ta kawo, musamman amfani da na’urar Virtual Reality (VR), yana mai cewa tsarin zai canza yadda ɗalibai ke koyon karatu.

Ya kara da cewa tsarin zai samar da fa’idodi da dama ga ɗalibai, malamai da makarantu saboda yana ƙara sha’awar koyo da koyarwa.

Sanata Shettima ya yi kira ga NEDC, Ma’aikatar Raya Yankunan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki su yi haɗin gwiwa don tabbatar da inganci da samun sakamako mai kyau a ayyukan su.

Shettima ya fadi shirin gwamnati a kan ma'aikata

A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce gwamnatin Najeriya ta na da sauye-sauye da za su inganta rayuwar ma'aikata.

Ya ce daga cikin shiryeshiryen, akwai tabbatar da cewa an fara biyan ma'aikatan gwamnatin kasar mafi karancin albashin N70,000, inda ya ce akwai wasu tsare-tsaren a gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.