Matsalar Tsaro: Gwamna Ya Bukaci Jiragen Yaki Su Rika Sintiri a Iyakokin Bauchi

Matsalar Tsaro: Gwamna Ya Bukaci Jiragen Yaki Su Rika Sintiri a Iyakokin Bauchi

  • Rahotanni sun nuna gwamna Bala Mohammed ya jaddada kudirin hadin gwiwa da hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya a Bauchi
  • Ya bukaci Rundunar Sojin Sama ta kara sintirin jiragen yaki, musamman a yankunan iyakokin jihar don hana miyagun laifuffuka
  • Shugaban Rundunar Ayyuka na Musamman na Sojin Sama da ke Bauchi, Eniobong Effiong, ya gode wa gwamnan bisa goyon bayan da yake ba su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Rundunar Ayyuka na Musamman na Sojin Sama da ke Bauchi, AVM Eniobong Effiong da ke shirin ritaya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bayyana shirinta a kan ma'aikata a Najeriya

Bauchi
Gwamnan Bauchi ya gana da tawagar sojin saman Najeriya. Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Source: Facebook

Hadimin Sanata Bala Mohammed a fannin yada labarai, Lawal Muazu Bauchi ne ya wallafa jawabin da gwamnan ya yi a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin ganawar, Gwamna Bala ya jinjinawa Effiong kan irin gudunmawar da ya bayar wajen inganta tsaro a lokacin da yake kan mukaminsa.

Bukatar inganta sintirin jiragen sama

Gwamna Bala Mohammed ya bukaci Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ta kara sintirin jiragen yaki, musamman a yankunan iyakokin jihar Bauchi, domin hana ayyukan bata gari.

Ya bayyana cewa hadin gwiwa tsakanin Sojin Sama da sauran hukumomin tsaro zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da dakile miyagun laifuffuka a jihar.

A cewar gwamnan:

"Dole ne mu kara kokari wajen kare mutanenmu daga ‘yan ta’adda da masu aikata laifuffuka.
Wannan shi ne dalilin da ya sa muke bukatar karin sintirin jiragen sama a iyakokinmu."

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da umarni a dauki ma'aikatan lafiya 150 aiki, an ji inda za a tura su

Gwamnan jihar Bauchi ya yabawa sojoji

A yayin taron, Gwamnan ya jinjinawa AVM Eniobong Effiong bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen samar da tsaro a Bauchi a lokacin da yake kan mukaminsa.

Gwamnan ya ce:

"Mun yaba da irin rawar da kuka taka wajen tabbatar da tsaro a Bauchi. Muna fatan za a ci gaba da kokari domin ganin an samar da ingantaccen tsaro a jihar."

Haka nan, Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya domin ganin an dakile ayyukan bata gari.

Jawabin Eniobong Effiong a madadin sojoji

A nasa bangaren, AVM Eniobong Effiong ya nuna godiyarsa ga Gwamna Bala bisa irin goyon bayan da yake bai wa Sojin Sama wajen gudanar da ayyukansu a Bauchi.

Eniobong Effiong ya ce:

"Muna godiya ga Gwamnatin Jihar Bauchi bisa hadin gwiwa da tallafin da take bamu wajen samar da tsaro.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya yi dabarar sanya Tinubu kashe Naira biliyan 33 a aikin titi

"Mun kudiri aniyar ci gaba da aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya a jihar da kasa baki daya."

Effiong ya tabbatar wa da Gwamna Bala cewa Rundunar Sojin Sama za ta ci gaba da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don ganin Bauchi ta kasance cikin kwanciyar hankali.

Sojoji sun yi fada da 'yan sanda a Delta

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta yi bayani kan hayaniya da aka yi da jami'anta da wasu 'yan sanda a jihar Delta.

Rahotanni sun nuna cewa an dauki matakin ladabtar da sojojin da suka yi fadan yayin da aka ba 'yan sandan da suka samu rauni kulawar lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng