Kamfanin Hada Motocin Dangote Ya Fara Aiki a Arewacin Najeriya

Kamfanin Hada Motocin Dangote Ya Fara Aiki a Arewacin Najeriya

  • Dangote ya dauki matakan mamaye kasuwar kera motoci a Najeriya, musamman a bangaren motocin kasuwanci da fasinja
  • Kamfanin ya fara hada sabbin nau'ikan motoci a masana'antunsa na Kaduna da Legas, ciki har da mota samfurin Peugeot 3008 GT
  • Masana'antar Dangote ta DPAN na kokarin fadada kasuwarsa ta hanyar bude sababbin wuraren saida motoci da gyara su a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Kamfanin Dangote ya kara matsa lamba kan manufarsa ta zama jagora a bangaren hada motoci a Najeriya.

Kamfanin ya riga ya dauki lasisin hada motocin Peugeot da Sinotruck a shekarun baya, tare da ci gaba da hada sababbin nau'ukan motoci a masana'antunsa na Kaduna da Legas.

Dangote
Dangote ya fara hada motoci a Kaduna. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a cikin wani sabon mataki, Dangote ya fara hada sabon nau’in Peugeot 3008 GT a masana’antar da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Majalisa: "Matasa sama da 500,000 a jihohin Arewa 2 sun rasa aikin yi"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na cikin kokarn Dangote kokarin farfado da shaharar motocin Peugeot da suka shahara a Najeriya a shekarun baya.

Peugeot 3008 GT ta shiga kasuwa

Kamfanin DPAN ya sanar da fara hada motoci samfurin Peugeot 3008 GT, wanda ke dauke da manyan injuna masu karko.

Haka zalika, sabon motar ta shiga jerin motocin Peugeot da ake kera a Najeriya, ciki har da Peugeot 301 Sedan da Peugeot 5008 SUV.

DPAN ya bayyana cewa hada Peugeot 3008 GT wani bangare ne na shirinsa na fadada nau’ukan motocin da ake kerawa a cikin gida, domin tabbatar da wadatar motocin Peugeot a Najeriya.

Karin motocin da Dangote zai samar

Baya ga Peugeot 3008 GT, DPAN ya sanar da kaddamar da Peugeot Landtrek 4×2, wata mota kirar Pickup.

Sabon ci gaban yana nuna cewa DPAN ya fara shiga kasuwar motocin kasuwanci manya domin ba da damammaki ga ‘yan kasuwa da masu bukatar irin wadannan motoci.

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya yi kokuwa da soja domin kwace bindiga a cikin daji

Shugaban kasuwancin DPAN, Umar Isa-Kaita, ya bayyana cewa kamfanin yana tattaunawa da kamfanonin hada motoci don fadada shirin sayar da Peugeot a fadin Najeriya.

DPAN zai dawo da martabar Peugeot

A cewar Daraktan DPAN, Ibrahim Isa Gachi, kamfanin na aiki tukuru don tabbatar da cewa Peugeot ta sake zama daya daga cikin manyan motocin da ake amfani da su a Najeriya.

Business Day ta wallafa cewa ya ce:

“Shirinmu shi ne mu ci gaba da kera sababbin motoci domin bai wa ‘yan Najeriya zabin da ya dace, kuma hakan zai kara farfado da kasuwar hada motoci a kasar.”

Kasancewar masana'antar Kaduna na iya hada motoci 120 a rana, DPAN na da niyyar kara habaka yawan motocin da ake kerawa, domin sake dawo da martabar Peugeot a Najeriya.

Cigaban da DPAN ya samu na daga cikin shirin hadin gwiwa da Kamfanin Dangote ya yi da gwamnatocin Kaduna, Plateau da Kebbi da kuma Stellantis wanda ke kula da Peugeot a duniya.

Kara karanta wannan

NNPCL ya shirya hadaka da Rahama Sadau, Adam Zango da jiga jigan Kannywood

Dangote ya rage farashin dizil

A wani rahoton, kun ji cewa matatar Dangote ta rage farashin man dizil a kasuwar Najeriya saboda wasu dalilai.

Rahoton Legit ya nuna cewa hakan na zuwa ne bayan Dangote ya sauke farashin man fetur a kwanakin baya saboda saukar farashin danyen mai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng