Tinubu ba Ya cikin Najeriya Yanzu Haka, An Ji Inda Shugaban Kasar Ya Tafi

Tinubu ba Ya cikin Najeriya Yanzu Haka, An Ji Inda Shugaban Kasar Ya Tafi

  • Shugaba Bola Tinubu ya isa Addis Ababa, babban birnin Habasha, domin halartar taron AU daga ranar 14 zuwa 18 Fabrairun 2025
  • Wakilan gwamnatin Habasha da wasu mukarraban gwamnatin Najeriya ne suka tarbi Shugaba Bola Tinubu a filin jirgin sama
  • An ce Tinubu zai gabatar da jawabi a taron AU na wannan shekarar nan da ya fi mayar da hankali kan tsaro, da hadin kan Afirka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ethiopia - Shugaba Bola Tinubu ya isa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, domin halartar taron shugabannin kasashen Afirka na AU.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara kan watsa labarai, ya sanar da isar Tinubu Habasha a cikin wata sanarwa a safiyar Juma'a.

Fadar shugaban kasa ta yi magana da Tinubu ya dura kasar Habasha
Tinubu ya dura kasar Habasha, zai gabatar da jawabi a taron AU. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya dura Addis Ababa domin taron AU

Sanarwar da hadimin Tinubu kan kafofin sadarwa, Temitope Ajayi ya wallafa a shafinsa na X ta ce taron AU zai gudana daga 14 zuwa 18 ga Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan

'Can ta matse musu': Ribadu ya fusata da aka wulakanta hafsan tsaron Najeriya a ketare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Eshetu Legesse, jami'ar gwamnatin Habasha, ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar da wakilin Najeriya a Habasha, Nasir Aminu suka tarbi Tinubu.

Sanarwar ta ce Ambasada Yusuf Tuggar ya yiwa Shugaba Tinubu bayanin taron da nasarorin diflomasiyya da suka samu har zuwa ƙarfe 2:00 na safiyar Jumma'a.

Nasarorin da Najeriya ta samu a AU

Ambasada Tuggar ya shaidawa Tinubu cewa an sake zaben Bankole Adeoye a matsayin kwamishinan AU na harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro.

Haka zalika, Tinubu ya ji labarin cewa Najeriya ta ci gaba da rike kujerarta a majalisar tsaro da zaman lafiya ta kungiyar AU.

Taron ya samu halartar ministocin kudi, tsaro, kasuwanci, jiragen sama, da sauran muhimman ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Tinubu zai dawo Najeriya ranar Litinin

Sanarwar ta ce taron AU na wannan shekara za a gudanar da shi ne karkashin taken: "Adalci ga Afirka da Mutanen Afirka ta hanyar biyan diyya."

Kara karanta wannan

Matakin da APC ta dauka kan 'ya'yanta da suka bauɗe, suke cin mutuncin Tinubu, Ganduje

Tinubu zai gabatar da jawabi a taron majalisar tsaro da zaman lafiya na AU, inda zai tattauna kan kalubalen tsaro da ake fuskanta a Afrika..

Shugaba zai halarci tarurruka kan samar da kudaden kiwon lafiya, kafa hukumar bashi ta Afirka, da taro kan sauyin yanayi; inda ake sa ran zai dawo Abuja ranar Litinin.

Tinubu ya gana da shugabannin Afrika

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya gana da shugabannin kasashen Afrika, inda suka tattauna kan matsalar taro a taron AU karo na 37.

Hakazalika, shugaban kasar ya samu damar halartar taron majalisar zartarwar AU karo na 44 wanda aka tattauna batutuwan da suka shafi ilimi a kasashen Afrika.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.