ATM: CBN Ya Toshe Hanyar da 'Yan Najeriya za Su Kaucewa Zare Musu Kudi ta Banki
- Babban Bankin Najeriya ya tabbatar da cewa za a rika cire N100 ga masu cire kudi har kasa da N20,000 a ATM din bankin da ba su da akawun
- Sabon tsarin kudi da CBN ya fitar zai fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2025, inda harajin zai shafi masu cire kudi a wasu bankuna ta na'urar ATM
- CBN ya yi karin haske a kan kudin da za a rika cirewa ne saboda tambayoyi da aka samu bayan fitar da sabon tsarin a makon da muke ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar da cewa za a rika cire N100 a matsayin haraji idan mutum ya cire kudi ko da kasa da N20,000 ne ta ATM din bankin da ba shi da asusu.

Kara karanta wannan
'Suna jawo bala'i': Basarake ya haramta ayyukan bokaye mata bayan kisan dan majalisa
Bankin ya yi karin haske ne kasancewar a farko ya ce za a rika cire N100 ne idan mutum ya zare N20,000 ko sama da haka ta ATM.

Asali: Getty Images
Punch ta wallafa cewa karin hasken na kunshe ne a wata takardar da CBN ya fitar a ranar Alhamis, inda aka fayyace sabon tsarin kudin da bankin ya sanya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dokar bankin CBN kan cire kudi ta ATM
Tsarin da CBN ya fitar ya nuna cewa wadanda ke cire kudi a ATM na bankin da suke da asusu ba za su biya haraji ba.
A farko, CBN ya sanar da cewa masu amfani da ATM na wani banki za su ci gaba da biyan N100 kan kowanne cire N20,000 da suka yi a ATM da ke harabar bankuna.
A gefe guda, masu amfani da ATM da ke wajen harabar bankuna, kamar wuraren kasuwanci, gidajen mai da sauran wurare, za su fuskanci karin kudi na har zuwa N500.
Karin haske da bankin CBN ya yi
CBN ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar haraji kan cire kudi kasa da N20,000 ne domin hana mutane raba kudin da za su rika cirewa da nufin kaucewa haraji.
Rahoton Nairametrics ya nuna cewa bankin ya ce:
“Za a ci gaba da karbar N100 kan kowanne cire kudi kasa da N20,000 daga bankin da mutum ba shi da asusu.
"Hakan na da nufin hana mutane raba kudin da za su cire don gujewa haraji.”
Haka zalika, CBN ya ce masu cire kudi sama da N20,000 daga bankin da ba su da asusu za su biya karin N100 kan kowanne karin N20,000 da suka cire.
Sauye-sauyen da aka yi a tsarin ATM
A baya, bankuna na bai wa abokan cinikinsu damar cire kudi sau uku kyauta a ATM na wasu bankuna a wata guda, amma daga 1 ga watan Maris, 2025, wannan dama ta kare.
Wannan sauyi zai iya kara kudin da masu amfani da ATM ke kashewa, musamman ga wadanda ke amfani da ATM na wasu bankuna a kai a kai.
Duk da haka, CBN ya bayyana cewa bankuna ba su da hurumin kara fiye da adadin da aka kayyade, amma za su iya rage kudin bisa tsarin kasuwancinsu.
CBN ya ba mutane shawari
CBN ya gargadi bankuna da kada su tilasta wa abokan cinikinsu cire kudi kasa da N20,000 matukar suna da isasshen kudi a asusun su.
Bankin ya ce duk wanda aka tilasta masa hakan zai iya kai rahoto zuwa sashen kare hakkin masu amfani da bankuna na CBN ta adireshin cpd@cbn.gov.ng.
Haka kuma, CBN ya shawarci ‘yan Najeriya da su fi amfani da ATM na bankunansu don rage harajin da za su rika biya.
Yadda CBN ya ci tarar bankuna a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa bankin CBN ya sanya tarar kudi sama da Naira biliyan 1 ga wasu bankuna a Najeriya.
Rahoton Legit ta tabbatar da cewa bankin CBN ya dauki matakin ne a kan bankunan da aka samu da laifin rashin samar da kudi ta ATM.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng