'Da Ya bi Shawara Ta da Bai Mutu Ya Bar Ni Gwauruwa ba': Matar Tsohon Gwamna

'Da Ya bi Shawara Ta da Bai Mutu Ya Bar Ni Gwauruwa ba': Matar Tsohon Gwamna

  • Uwargidar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta koka kan yadda marigayin bai ji shawarwarin da ta ba shi ba
  • Betty Akeredolu ta ce marigayi tsohon gwamnan ba zai mutu ba da ya saurare ta game da jinyar ajali da ya yi fama da ita
  • Ta ce mijinta ya zabi maganin gargajiya maimakon jinya ta likitoci, wanda ya jawo ajalinsa a sakamakon cutar sankarar mafitsara
  • Betty, wadda ta tsira daga cutar sankarar mama, ta ce bai yiwuwa a danganta kansa da matsalolin tsafi ko al'amarin ruhaniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Abeokuta, Ondo - Matar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta sake karin haske bayan mutuwar mijinta game rashin lafiyarsa.

Betty Akeredolu ta ce da mijinta ya saurare ta game da maganin cutar kansa, da ba zai mutu ba.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Matar tsohon gwamna ta koka kan kin bin shawarinta da ya yi
Matar marigayi Rotimi Akeredolu ta ce da tsohon gwamnan ya bi shawarinta da bai mutu ba. Hoto: Betty Akeredolu.
Asali: Facebook

Yadda Betty ta yi fama da sankarar mama

Betty ta bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ta yi da Olumide Akinrinlola da Vanguard ta bibiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar da aka gano tana da sankarar mama shekaru 27 da suka wuce, ta ce yanke shawarar neman maganin likita maimakon na gargajiya ya taimaka mata.

Betty ta ce Akeredolu mutum ne mai bin addini, amma ita “an halicce ta daban” kuma ba ta jin kunyar fadin hakan.

Betty ta fadi silar mutuwar gwamnan Ondo

Da aka tambaye ta ko ta ki amincewa da addu'o'i ko taimakon addini lokacin da Akeredolu ke fama da kansa, ta ce:

“Me suka tsinana?
“Daga hawa duwatsu, tawul da aka ce an albarkace su, ruwa, man zaitun, da addu'o'i kamar masu aljanu?
“Da Aketi ya saurare ni, da ba zan zama gwauruwa ba.”
"Idan batun addini ne, ina gaya wa mutane su tsaya kan tafarkinsu, ni kuma na tsaya kan nawa."

Kara karanta wannan

"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027

Betty ta soki bin tsarin gargajiya a neman lafiya

Betty, wacce ta tsira daga cutar sankarar mama, ta bayyana cewa ta fahimci yadda cutar take saboda ilimin kimiyyar da ta samu.

Ta ce ba za ta taba amincewa cewa tsafi ko al’amuran ruhaniya ne ke haddasa cutar kansa ba, jaridar Punch ta ruwaito.

An caccaki matar marigayi tsohon gwamna

A baya, kun ji cewa yan Najeriya sun caccaki matar marigayi tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu kan kalamanta na cin zarafin yan kasar.

An ce Betty Akeredolu ta yi rubutu a shafin X inda ta kira Najeriya da gidan 'zoo' da bai yi wa yan kasar dadi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.