Gwamnoni 6 Sun Shirya Fito na Fito da Ƴan Ta'adda, Za a Kafa Babbar Rundunar Tsaro

Gwamnoni 6 Sun Shirya Fito na Fito da Ƴan Ta'adda, Za a Kafa Babbar Rundunar Tsaro

  • Gwamnonin Kudu maso Yamma sun yanke shawarar kafa babbar rundunar hadin gwiwa ta tsaro don magance matsalar tsaro a yankin
  • Kungiyar gwamnonin ta amince da amfani da fasahar zamani don inganta harkar tsaro tare da kafa cibiyoyin abinci na hadin gwiwa
  • Gwamnonin sun jaddada hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro na jihohi da na tarayya domin inganta tattara bayanan sirri da tsaro a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Gwamnonin Kudu maso Yamma sun yanke shawarar kafa tawagar hadin gwiwa don yaki da matsalar tsaro da ke karuwa a yankin.

Gwamnonin, karkashin inuwar SGF, sun amince su kafa cibiyoyin abinci na hadin gwiwa don magance hauhawar farashin kayan abinci.

Gwamnan Legas ya yi magana da gwamnonin Kudu maso Yamma suka shirya samar da rundunar tsaro
Gwamnonin Kudu maso Yamma za su samar da rundunar tsaro don yaki da 'yan ta'adda. Hoto: @DapoAbiodunCON
Asali: Twitter

Taron ya gudana ne a gidan gwamnatin Legas da ke Alausa, Ikeja, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da umarni a dauki ma'aikatan lafiya 150 aiki, an ji inda za a tura su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma ne ya jagoranci taron.

Gwamnonin Kudu za su kafa rundunar tsaro

Sanwo-Olu ya bayyana cewa matakan sun zama wajibi saboda barazanar tsaro da ke iya kawo cikas ga zaman lafiya da cigaban yankin.

Gwamnan ya ce:

"Kungiyar ta amince da nada mashawarta na musamman kan tsaro a kowace jiha da kuma kafa rundunar tsaron hadin gwiwa don sa ido."

Sanwo-Olu ya kara da cewa za a yi amfani da fasahar zamani, ciki har da dabarar sa ido ta sama, domin inganta ayyukan tsaro.

Haka kuma, kungiyar ya yanke shawarar kara karfin tattara bayanan sirri ta hanyar hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaron jihohi da na kasa.

Gwamnoni 6 sun shirya tunkarar matsalolinsu

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Lucky Aiyedatiwa (Ondo), Dapo Abiodun (Ogun), Seyi Makinde (Oyo), Ademola Adeleke (Osun) da Biodun Oyebanji (Ekiti).

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ta nemi ba ni rashawar N5bn," Ɗan takarar shugaban ƙasa

Sanwo-Olu ya bayyana cewa manufar taron ita ce tattauna manyan batutuwa da suka shafi yankin, ciki har da harkar noma da yadda za a samu isasshen abinci.

Gboyega Akosile, mai magana da yawun Sanwo-Olu, ya ce taron ya mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi makomar hukumar bunkasa Kudu maso Yamma.

Gwamnonin sun kuma jaddada muhimmancin hada kai tsakanin jihohi don tabbatar da tsaron abinci da kawo ci gaba mai dorewa ga yankin.

Gwamnonin Kudu sun kawo tsarin samar da abinci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnoni shida na jihohin Kudu maso Yamma sun umarci ma'aikatun noma na jihohinsu da su kawo dabarun samar da abinci.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya shaida cewa ba za su yarda da hauhawar farashin abinci ba, don haka za su dauki matakan wadatar da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.