Majalisa: "Matasa Sama da 500,000 a Jihohin Arewa 2 Sun Rasa Aikin Yi"
- Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Dr. Tajudeen Abbas, ya koka kan rushewar masana’antar sarrafa yadi a jihohin Kano da Kaduna
- Ya ce wannan lamari ya jawo babbar asara , musamman ta aikin yi ga mazauna jihohin biyu ganin yadda aka rasa ayyuka 500,000
- Rt. Hon. Abbas ya bayyana fatan sabuwar hukumar farfado da Arewa maso Yamma (NWDC) za ta yi abin da ya dace a kan matsalar yankin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban Majalisar Wakilai, Dr. Tajudeen Abbas, ya koka kan asarar fiye da ayyuka 500,000 sakamakon rushewar masana’antun samar da yadi, a jihohin Kano da Kaduna a shekarun baya.
Ya bayyana damuwarsa ne yayin kaddamar da Kwamitin Majalisa kan Hukumar Raya Arewa Maso Yamma (NWDC) jiya a zauren majalisa a jiya.

Asali: Facebook
The Guardian ta ruwaito cewa shugaban majalisar ya ce masana’antar yadi da ta kasance ginshikin tattalin arziki a shekarun 1980, yanzu tana daukar ƙasa da mutum 20,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya danganta rushewar masana'antar da raunin manufofi da kuma ƙaruwar matsalar tsaro, wanda yanzu ya ke zama babbar barazana ga tattalin arziki.
Shugaban majalisa na son a inganta Arewa
Daily Post ta wallafa cewa Tajudeen Abbas, ya ce matsalar rashin aiki na kara kamari ganin yadda aka yi watsi da Arewa na tsawon lokaci.
Ya ce wannan, da lalacewar muhalli sun daƙile bunkasar tattalin arziki da kuma rage hanyoyin samun abin dogaro da kai a shiyyar.
Majalisa ta ba da shawarar inganta Arewa
Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ce Hukumar Raya Arewa Maso Yamma (NWDC) ta na da damar magance wadannan matsaloli ta hanyar ingantattun tsare-tsare.
Shugaban majalisar ya bukaci NWDC da ta gudanar da cikakken bincike kan bukatun yankin don gano muhimman wuraren da suka fi bukatar dauki.
Ya ce:
Wannan bincike zai zama ginshikin samar da tsare-tsaren ci gaba na shekaru 10, wanda zai kunshi ainihin manufofi da dabarun aiwatarwa.
Shugaban Majalisar ya bukaci NWDC da ta rungumi hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi, sarakunan gargajiya, kungiyoyin farar hula, da bangaren masu zaman kansu.
Ya jaddada cewa hadin gwiwa ne zai tabbatar da cewa duk wani shiri da aka aiwatar zai kasance mai dorewa kuma mai inganci.
"Akwai kura-kurai a ƙudirin haraji," Ɗan majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan majalisar tarayya mai wakiltar Jibia/Kaita a majalisar wakilai ya ce akwai kura-kurai da dama nannaɗe a cikin ƙudirin haraji.
Hon. Sada Soli, wanda ya bayyana haka, ya tabbatar da cewa wadanda su ka rubuta wa Bola Tinubu kudirin ba su yi aiki mai inganci ba, inda ya nemi a gyara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng