Rikita Al’adun Hausawa: Kotu Za Ta Yi Zama kan Karar da Aka Shigar da Arewa24
- Babbar Kotun Tarayya za ta saurari shari’ar NBMOA da Arewa24 a Abuja, bisa zargin gudanar da ayyuka ba tare da lasisi ba a Najeriya
- Shugaban NBMOA, Alhaji (Dr.) Ahmed Ramalan, ya ce ƙungiyar na son tabbatar da bin ƙa’idojin yaɗa labarai da tabbatar da adalci a fannin
- Shari’ar na da alaƙa da hukumomi da kamfanoni da dama, wanda zai iya yin tasiri ga tsarin yaɗa labarai a Najeriya, ana jiran hukuncin alkali
- Wannan na zuwa ne yayin da Arewa24 ta yi bikin cika shekaru 10 da fara yada shirye-shirye a Yulin 2024, inda ta sake kawo wasu tsare-tsare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya a Abuja za ta ci gaba da sauraren shari’ar da ke tsakanin kungiyar masu watsa labarai ta Arewa, NBMOA da gidan talabijin na Arewa24.

Kara karanta wannan
"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027
Ana zargin tashar Arewa24 da gudanar da ayyukan yaɗa labarai ba tare da samun lasisin da ya dace ba da kuma bin ka'idojin doka.

Asali: Facebook
Musabbabin maka Arewa24 a gaban Kotu
Shugaban kwamitin amintattu na NBMOA, Alhaji (Dr.) Ahmed Tijjani Ramalan shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shigar da ƙarar ne tun a watan Nuwambar 2024, inda aka haɗa hukumomi da kamfanoni kamar NBC, ARCON, FCCPC, MultiChoice Nigeria da StarTimes.
Masana da masu ruwa-da-tsaki a fannin yaɗa labarai na sa ido kan sakamakon shari’ar, domin zai iya shafar tsarin yaɗa labarai a Najeriya.
NBMOA ta bayyana damuwarta kan yadda Arewa24 ke gudanar da shirye-shiryenta ba bisa ƙa’ida ba, wanda ke yin tasiri ga harkar yaɗa labarai.
Ahmad Ramalan ya fadi matakin da suke dauka
Ahmad Ramalan ya jaddada himmatuwar kungiyar wurin kiyayewa da kuma tabbatar da ka'idojin yada labarai.
Ahmed Tijjani Ramalan ya ce:
“Manufarmu ita ce tabbatar da adalci da daidaito a fannin yaɗa labarai."
Zafafan shirye-shirye da Arewa24 ta kawo
A baya, kun ji cewa a watan Yunin 2024, tashar talabijin din Arewa24 ta yi bikin cika shekaru 10 da fara yaɗa shirye shirye a jihar Kano.
Biyo bayan haka, tashar ta fitar da sababbin shirye shirye guda uku domin bunkasa alakarta da al'umma Arewacin Najeriya.
Daga cikin shirye-shiryen da za su rika gudana a tashar talabijin na Arewa24 yanzu akwai Arewa Gen-Z da kuma sauyin yanayi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng