Mutuwar Ɗan Majalisa Ta Bar Gwamna a Matsala, Mutane Sun Yi Masa Kaca Kaca

Mutuwar Ɗan Majalisa Ta Bar Gwamna a Matsala, Mutane Sun Yi Masa Kaca Kaca

  • Kisan ɗan Majalisa mai wakiltar Onitsha, Hon. Justice Azuka ya harzuƙa mutanen mazaɓarsa, sun caccaki Gwamna Charles Soludo
  • Al'ummar Onitsha sun nuna ɓacin ransu kan lamarin, suna cewa Gwamna Soludo ya gaza cika alƙawurran ya ɗaukar masu lokacin zabe
  • A watan Disamba, 2024, wasu miyagn ƴan bindiga suka sace ɗan Majalisar ana gobe kirismeti, bayan kwanaki 40 aka gano gawarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Al’ummar mazaɓar Onitsha da ke Anambra sun soki Gwamna Charles Soludo kan sacewa da kisan dan majalisar jiha, Hon. Justice Azuka.

A ranar 24 ga Disamba, 2024, wasu ‘yan bindiga suka sace Hon. Azuka, wanda ke wakiltar Onitsha a majalisar dokokin jihar Anambra.

Gwamna Soludo.
Mutanen Onitsha sun caccaki Gwamna Soludo kan kisan ɗan Majalisa Hoto: Charles Chikwuma Soludo
Asali: Facebook

Bayan kwanaki 40 da yin garkuwa da shi, wata tawagar jami’an tsaro ta gano gawarsa a gadar Neja ta biyu da ke Onitsha, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

NNPCL ya shirya hadaka da Rahama Sadau, Adam Zango da jiga jigan Kannywood

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane sun caccaki Gwamna Charles Soludo

A yayin taron da suka gudanar a garin Onitsha a ranar Litinin, al’ummar yankin sun bayyana fushinsu kan yadda rashin tsaro ke kara tabarbarewa a karkashin gwamnatin Soludo.

Sun bukaci gwamnatin Anambra ta fadi matakan da take dauka domin shawo kan matsalar tsaro, musamman bayan kisan Azuka, wanda ya zama na biyu a cikin shekara daya.

Cikin wata sanarwa da mai hadimin sarkin Onitsha, Osita Anionwu, ya fitar a ranar Talata, mutanen sun nuna takaicinsu da yadda Gwamna Soludo ya gaza cika alƙawurran da ya ɗauka.

Jama'an Onitsha sun soki jami'an tsaro

Har ila yau, muzauna Onitsha sun yi tir da wani bidiyo da jami’an tsaro suka wallafa a shafukan sada zumunta, wanda ke nuna wani da ake zargi da hannu a kisan Azuka.

“Ya kamata gwamnati ta maida hankali wajen hana irin wadannan manyan laifuka da tabbatar da adalci, maimakon yayata bidiyon da ke tada hankali,” in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Alamu sun ƙara karfi, gwamna na shirin neman takarar shugaban ƙasa a 2027

Sun kuma caccaki hukumomin tsaro da kasa gano inda Azuka yake tsawon kwanaki 40, tare da zargin gwamnatin Soludo da rashin tuntubar dangin marigayin da kuma al’ummar yankin yadda ya kamata.

Ƴan bindiga sun karɓi N100m a Anambra

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindigar da suka kashe ɗan Majalisa a Anambra sun karɓi kudin fansa Naira miliyan 100 bayan sace shi.

Wannan bayanai na fitowa ne bayan dakarun ƴan sanda sun cafke waɗaɓda ake zargi da hannu a kisan ɗan Majalisar, Justice Azuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel