Tushen Wutar Lantarkin Najeriya Ya Samu Matsala, An Fadi Jihohin da Abin Ya Shafa
- Tushen wutar lantarkin Najeriya ya samu matsala da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar Laraba, wanda ya jawo daukewar wuta a Abuja
- Yawan karfin wutar da ake samarwa ya ragu daga 4,064.70MW zuwa 1,222.78MW, wanda ya shafi kamfanonin wuta na AEDC da IKEDC
- Kamfanonin rarraba wutar sun sanar da cewa sun fara aikin maido da wuta yayin da aka ce matsalar ta shafi har da yankunan Legas
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wasu sassan Najeriya sun fuskanci katsewar wutar lantarki a ranar Laraba bayan wata matsala ta faru a kan tushen wutar ƙasar.
Bayanan da aka samu daga mai kula da tsarin samar da lantarki (ISO) sun nuna cewa yawan karfin wutar da ake samarwa ya sauka daga 4,064.70MW zuwa 1,222.78MW.

Asali: Getty Images
Kamfanonin lantarki na Ikeja (IKEDC) da na Abuja (AEDC) sun ce matsalar ta faru da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar Laraba, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dauke wuta a Abuja da Legas
Kamfanin AEDC ya bayyana cewa wannan matsala ta jawo daukewar wutar lantarki a dukkan yankunan da suke karkashinsa.
Yankunan da kamfanin AEDC ke kula da samar da wutarsu su sun haɗa da Abuja, Kogi, Neja da Nasarawa.
“Mun yi baƙin cikin sanar da ku cewa matsala ta faru a kan tushen wutar ƙasar da misalin ƙarfe 11:34 na safe, wanda ya janyo daukewar wuta,” inji AEDC.
Kamfanin ya ce an fara maido da wuta a hankali tare da haɗin gwiwar hukumomin da abin ya shafa yayin da ake kokarin ganin an maido wutar gaba ɗaya.
TCN ya hasasho yawaitar matsalar wuta
A bangare daya kuma, kamfanin IKEDC ya sanar da cewa an samu irin wannan matsala daidai wannan lokaci, wanda ya shafi dukkan hanyar samar da wuta a yankunansa.
Kamfanin ya ce ana ci gaba da aiki tare da hukumomin da abin ya shafa don maido da wutar lantarki cikin gaggawa.
A watan Nuwamban 2024, kamfanin TCN ya yi gargadin cewa matsalolin lalacewar tushen wutar ƙasa na iya ci gaba da faruwa, amma ana kan gyara.
Kamfanin ya roki haɗin kan jama’a yayin da yake kokarin tabbatar da maido da tsarin yadda ya kamata.
'Yan ta'adda sun farmaki turken wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya ce 'yan ta'adda sun kai hari kan turken wutar Lokoja-Gwagwalada.
TCN ya ce 'yan ta'addar sun sace igiyoyin aluminium guda biyu wanda janyo cikas ga samar da wuta a Abuja, amma dai injiniyoyi na aikin gyarawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng