Gwamnatin Zamfara Ta Sake Fayyace Matsayarta kan Sulhu da 'Yan Bindiga
- Gwamnatin jihar Zamfara ta fito ta sake bayani kan matsayarta dangane da yin sulhu da ƴan bindiga masu tayar da ƙayar baya
- Ta bayyana cewa jar yanzu Gwamna Dauda Lawal yana kan matsayarsa ta cewa ba zai hau kan teburin sulhu da ƴan bindiga ba
- Wata sanarwa da mai maganan da yawun gwamnan ya fitar, ta nuna cewa ba a fahimci kalaman Dauda Lawal a wata hira da ya yi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta sake bayyana matsayarta kan yin sulhu da ƴan bindiga.
Gwamnatin ta Zamfara ta yi watsi da yiwuwar yin sulhu da ƴan bindiga don dawo da zaman lafiya a jihar ta yankin Arewa maso Yamma.

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Ana zargin gwamna ya ɗirkawa fitacciyar jaruma ciki a Najeriya, gaskiya ta bayyana
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamnatin ta ce kan sulhu da ƴan bindiga?
Gwamnatin ta ce ba a fahimci abin da Gwamna Dauda Lawal ya faɗa ba a yayin hirar da aka yi da shi a ƙarshen makon jiya.
A cewarsa, wasu kafafen yaɗa labarai sun fassarar hirar da wata manufa ta yaudara, domin karkatar da hankalin jama’a game da matsayin gwamnatin jihar kan sulhu da ƴan bindiga.
"Matsalar ƴan bindiga ta kasance babban abin damuwa ga al'ummar jihar Zamfara, yankin Arewa maso Yamma, da ma ƙasa baki ɗaya na tsawon shekaru."
"Wannan ne ɗaya daga cikin dalilan da suka sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a lokacin yaƙin neman zaɓensa kafin zaɓen 2023 cewa zai ba da fifiko ga harkar tsaro, inda ya sha alwashin ɗaukar matakai don magance matsalar."
"Gwamna Lawal ya tabbatar da cika wannan alƙawari, kuma ana ganin alamun nasara a aikace."
"Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta ba tsaron jihar Zamfara muhimmanci matuƙa, kuma tun daga farko ta ɗauki matsayar cewa yin sulhu da ƴan bindiga ba shi ba ne mafita."

Kara karanta wannan
Gwamna ya yi hangen nesa, ya fadi abin da sojoji suke bukata don magance rashin tsaro
"A cikin hirarraki daban-daban da ya yi da kafafen yada labarai, gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin jihar Zamfara ba za ta yi sulhu da ƴan bindigan da ke addabar jihar ba."
"Dole ne a fayyace cewa matsayin Gwamna Dauda Lawal yana nan daram a kan wannan matsayar. Babu wata gwamnati da za ta zauna teburin sulhu da masu kisan kai."
"Hirar Gwamna Dauda Lawal da BBC Hausa ta nuna cewa har yanzu yana nan a kan matsayarsa."
"Tun farko, ya jaddada cewa idan ana buƙatar wata tattaunawa, dole ne ƴan bindigan su ajiye makamansu su tuba ba tare da kafa wani sharaɗi ba."
- Sulaiman Bala Idris
Ƴan bindiga sun kafa sabon sansani a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ƙarƙashin jagorancin Dan Sa'adi, sun kafa sabon sansani a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun kafa sansanin ne a ƙaramar hukumar Kauran Namoda, wanda hakan ya jefa al'ummar yankin cikin damuwa da firgici.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng