Hisbah Ta Karrama Dangin da Su ka Ladabtar da Fitaccen Dan Tiktok

Hisbah Ta Karrama Dangin da Su ka Ladabtar da Fitaccen Dan Tiktok

  • Hukumar Hisbah ta Kano ta karrama iyalan Alhaji Ya’u Kura bisa matakin ladabtar da Yahaya America kan yada abubuwan batsa a tiktok
  • A taron karrama iyalan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yaba bisa yadda su ka taimaka wajen dawo da dan uwansu kan turbar tarbiyya
  • Sheikh Daurawa ya bayyana cewa Alhaji Ya’u Kura ya bar zuri’a mai addini da mutunci, wadanda su ka dauki matakin ladabtar da dayansu
  • Ya ce irin wannan mataki da ya yi karanci a cikin al'umma ne ya haddasa yawaitar matasa masu badala a shafukan sada zumunta da ake da su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta Kano, ta karrama iyalan Alhaji Ya'u Kura bisa yadda su ka dauki matakin ladabtar da dan uwansu da ake kira Yahaya America.

Kara karanta wannan

Arewa: El-Rufa'i ya aika gargadi ga APC da Tinubu kan zaben 2027

Matasahin, ya shahara a shafukan sada zumunta, musamman na Tiktok, inda ya ke yada kalaman batsa tare da wasu hirarraki da su ka saba da koyarwar addinin Musulunci.

Daurawa
Hisbah ta karrama 'yan uwan fitaccen dan tiktok Hoto: Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

A bidiyon da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya yabi 'yan uwan Yahaya 'America' wajen saita dan uwansu a kan turbar addinin Musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi addu'a ga Alhaji Ya'u Kura, ganin yadda ya bar zuri'a ta gari da ke lura da halin da 'yan uwansu ke ciki, domin dawo da su kan hanyar tarbiyya da aka dora su a kai.

Hisbah ta karrama 'yan uwan dan Tiktok

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa iyalan Alhaji Ya'u Kura saboda yadda su ka nuna cewa har yanzu akwai mutane masu mutunci da tarbiyya kasar nan.

A taron karramawar, Sheikh Daurawa ya ce:

"Alhaji Ya'u Kura, Allah Ya jikansa da rahama. Wannan bawan Allah ya na da zuri'a masu tarbiyya, masu addini. Wadanda daya daga cikinsu ya aikata abin da bai dace ba, su ka taru su ka ladabtar da shi.

Kara karanta wannan

"Dalilina na sukar BolaTinubu a baya," Hadimin shugaban kasa

Shugaban hukumar ta Hisbah ya ce wannan abu da su ka aikata, ya tabbatar da cewa har yanzu akwai burbushin mutunci a tarbiyya a cikin al'umma.

Hisbah ta jinjina ladabtar da dan tiktok

Hukumar Hisbah ta Kano ta mika lambar girmamawa ga iyalan Alhaji Ya'u Kura, inda aka gayyaci wasu daga cikin manyan da su ka ladabtar dan uwansu.

Sheikh Daurawa :

"Mun gayyato yayyansa, akwai Alhaji Haruna Ya'u Kura, akwai Alhaji Abubakar Ya'u Kura, Allah ya saka maka da alheri, akwai Hajiya Saude Ya'u Kura."

Ya bayyana cewa wandannan mutane sun yi abin koyi, wanda da ana daukar irin wannan mataki a cikin al'umma, da an samu raguwar tabara a tsakanin matasa.

Hisbah ta yaba wa 'yan uwan dan tiktok

A baya, kun ji cewa Shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana godiyarsa bisa matakin da iyalan Alhaji Ya'u Kura su ka dauka na saita dan uwansu a hanya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe ta fusata, an ba da umarnin farauto makasan malamin addini

Shehin malamin ya jaddada cewa irin wannan mataki shi ne abin da ake bukata a cikin kowace al’umma da gida don dakile yaduwar badala, wanda hakan zai inganta rayuwar Musulmi baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.