Gaskiya Ta Fito da Aka Fara Yaɗa Labarin Allah Ya Yi wa Sarkin Mai Martaba Rasuwa

Gaskiya Ta Fito da Aka Fara Yaɗa Labarin Allah Ya Yi wa Sarkin Mai Martaba Rasuwa

  • Sarkin Ugbo da ke ƙaramar hukumar Ilaje a Ogun, mai martaba Frederick Obateru Eniolorunda Akinruntan ya musanta rahoton cewa ya rasu
  • Basaraken ya shaidawa manema labarai ta wayar tarho a Akure, babban birnin jihar Ogun cewa yana nan a raye kuma cikin ƙoshin lafiya
  • Ya bayyana cewa a al'adar yarbawa raɗe-raɗin mutuwa alama ce ta tsawon rai, ya kwantar da hankulan mutanen masarautarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun - Sarkin Ugbo na masarautar Ugbo da ke karamar hukumar Ilaje a Jihar Ondo, Oba Frederick Obateru Eniolorunda Akinruntan, ya karyata jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya rasu.

Mai martaba sarkin ya musanta rahoton ya rasu, yana mai cewa yana nan cikin koshin lafiya.

Frederick Obateru Eniolorunda Akinruntan.
Sarki a Ogun, Iba Fedrick Obateru ya musanta raɗe-raɗin da ake cewa Allah ya masa rasuwa Hoto: Prince Abayomi Babatunde
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa baaraken ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho a Akure, babban birnin jihar Ogun yau Talata.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisa ya fito ya faɗi gaskiya, ya bayyana kuɗin da aka tura wa ƴan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki ya musanta labarin rasuwarsa

Basaraken, wanda ke da matsayi na farko a masarautar, ya ayyana wannan jita-jita da ke yawo a shafukan sada zumunta a matsayin “albarka da dogon rai.”

Oba Frederick Akinruntan ya tabbatar wa al'ummarsa da cewa lafiyarsa kalau babu abin da ke damunsa.

Ya bayyana hakan ne lokacin da lauya kuma shugaban kungiyar Afenifere, Cif Sola Ebiseni, ya kira shi ta waya kuma ya sa shi tattaunawar tarho kai tsaye da manema labarai.

"Ina nan cikin ƙoshin lafiya" - Sarkin Ugbo

Basaraken, wanda fitaccen dan kasuwar mai ne kuma shi ne wanda ya kafa kamfanin Obat Oil, ya ce:

“Ina cikin koshin lafiya. Na samu kira da dama daga sassa daban-daban na duniya, musamman daga jihar Ondo, kan labarin rasuwata.
Lauyana ya ba ni shawarar in yi magana da ku domin karyata wannan mummunar jita-jita, ina nan a raye.
“Tabbas, na yi tafiya don hutu na kankanin lokaci, kuma zan dawo gida nan ba da jimawa ba. A al’adar Yarbawa, irin wannan jita-jita na nufin albarka da dogon rai. Olugbo yana nan da ransa, kuma yana cikin koshin lafiya.”

Kara karanta wannan

Mummunar rigima ta kaure tsakanin ƙungiyoyi 2 kan 'kuɗi', an kashe mutane sama da 10

Gwamnan Ogun ya yi alhinin rasuwar sarki

A wani labarin, kun ji cewa rasuwar sarkin Iperu-Remo, Oba Adeleke Adelekan Idowu-Basi ya girgiza mai girma gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun.

A wata sanarwa da ya fitar, Gwamna Abiodun ya bayyana marigayin a matsayin shugaba nagari da ya kawo zaman lafiya da ci gaban yankinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel