Ta Faru Ta Kare: Kamfanin MTN Ya Kara Kudin Data, Ya Saki Sabon Farashi

Ta Faru Ta Kare: Kamfanin MTN Ya Kara Kudin Data, Ya Saki Sabon Farashi

  • Kamfanin sadarwa na MTN ya fara yin gaba wajen aiwatar da ƙarin kuɗin kira da data wanda hukumar NCC ta amince da shi
  • MTN ya fara aiwatar da ƙarin da ake ganin ya zarce kaso 50% kan kuɗin data, inda ya fitar da sabon farashi ga ƴan Najeriya
  • Sauran manyan kamfanonin sadarwa na Airtel da Glo ba su fara aiwatar da tsarin ba wanda zai sanya a ƙara yawan kuɗin da ake kashewa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban kamfanin sadarwa mafi girma a Najeriya, MTN, ya fara aiwatar da ƙarin farashin kuɗin data.

Kamfanin na MTN ya fara aiwatar da ƙarin da hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da shi a watan Janairun 2025.

MTN ya kara kudin data
MTN ya kara kudin data ga 'yan Najeriya Hoto: Delmaine Donson
Asali: Getty Images

Duk da cewa wannan karin farashi yana shafar tsarin sababbin farashin data, bai shafi kudin kiran waya da sakon SMS ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Shirin ƙarin kuɗin kira da sayen data a Najeriya ya gamu da cikas, Majalisa ta tsoma baki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta ce wani babban jami’in kamfanin MTN, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da hakan yayin wata tattauna ranar Talata, 11 ga watan Fabrairun 2025.

Ƙarin da kamfanin na MTN ya yi wanda ya shafi kuɗin data, bai fara aiki ba a kan kuɗi kira da tura saƙo.

"Eh, mun fara sabunta farashinmu. Amma muna yin hakan a hankali, kuma ba mu kammala na komai da komai ba."

- Wani jami'in MTN

Sabon farashin datan kamfanin MTN

Binciken da aka yi a ranar Talata ya nuna cewa ƙarin farashin ya shafi wasu manyan tsare-tsaren data na kamfanin MTN.

Tsarin 1.5GB na wata guda, wanda a baya ake siyarwa a N1,000, yanzu an sauya shi da 1.8GB, inda kuɗinsa suka kai N1,500.

Tsarin 15GB ya ƙaru daga N4,500 zuwa N6,500, tsarin 20GB yanzu ya koma N7,500, maimakon N5,500 da ake siyansa a baya.

Tsarin 600GB na tsawon kwanaki 90 ya tashi daga N75,000 zuwa N120,000. Tsarin 1.5 Terabyte (TB) na tsawon kwanaki 90 ya ƙaru daga N150,000 zuwa N240,000.

Kara karanta wannan

CBN ya kawo sabon tsarin cire wa 'yan Najeriya kudi wajen aiki da ATM

Glo da Airtel ba su ƙara farashinsu ba

Duk da cewa MTN ta fara aiwatar da wannan sabon tsarin, bincike ya nuna cewa kamfanonin Airtel da Glo ba su yi ƙarin farashin ba tukuna.

A ranar 20 ga watan Janairu, hukumar NCC ta amince da ƙarin farashin kuɗin kira da data a faɗin ƙasar nan.

Hukumar NCC ta bayyana cewa ta amince da ƙarin ne sakamakon ƙaruwar kuɗin da kamfanonin sadarwa ke kashewa wajen gudanar da ayyukansu da kuma buƙatar tabbatar da ɗorewar masana'antar a Najeriya.

Kotu ta hukunta kamfanin MTN

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta hukunta kamfanin sadarwa na MTN bayan an shigar da shi ƙara a gabanta.

Kotun ta ci tarar N15m ga kamfanin sadarwa na MTN kan ƙarar da wani abokin hulɗa ya shigar kan cire masa kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng