Gwamna Ya Fara Gyara, Ya Tattara Shugabanni 21 Ya Sallame Su daga Aiki Nan Take
- Gwamna Nasir Idris ya kori shugabannin hukumomin ilimi 21 watau ES na kananan hukumomin Kebbi, ya gode masu bisa gudummuwar da suka bayar
- Sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Yakubu Bala Tafida ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Birnin-Kebbi
- Gwamnan ya umarci dukkan waɗanda matakin ya shafa su mika ragamar jagoranci ga dataktocin gudanarwa na hukumominsu, ya masu fatan alheri
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu, ya sallami dukkan shugabannin hukumomin ilimi na kananan hukumomin 21 da ke faɗin jihar.
Gwamna Idris ya kori shugabannin su 21 a wani yunƙuri na gyara ɓangaren ilimi a faɗin jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Asali: Facebook
Sanarwar sallamar ta fito ne daga hannun Sakataren Gwamnatin jihar (SSG), Yakubu Bala Tafida, kamar yadda Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Nasir ya fara gyara ɓangaren ilimi
A sanarwar da ya rabawa manema labarai da yammacin ranar Litinin a Birnin Kebbi, sakataren gwamnatin Kebbi ya ce matakin korar zai fara aiki ne nan take ba tare da jinkiri ba.
Gwamnan Kebbi ya yaba da gudunmuwar da wadannan shugabanni suka bayar wajen ci gaban ilimi a yankunansu, tare da yi musu fatan alheri a harkokinsu na gaba.
Sakataren gwamnatin ya bayyana cewa waɗanda aka sauke sun taka rawar gani wajen inganta harkar ilimi a kananan hukumomi kafin yanzu da aka sallame su daga aiki, rahoton Channels tv.
Gwamna ya umarci su miƙa ragama
Yakubu Bala ya ce an umarci waɗanda lamarin ya shafa da su mika ragamar mulki ga daraktocin gudanarwa a ofisoshinsu na kananan hukumominsu.
Wannan mataki na sauke su daga mukamansu na iya kasancewa wani yunkuri na sake fasalin tsarin ilimi a matakin kananan hukumomi domin tabbatar da ingancin ilimi a Kebbi.

Kara karanta wannan
Gwamna ya gano badaƙalar kudi, ya dakatar da kwamishina da shugaban hukuma nan take
Duk da cewa gwamnatin Kebbi ba ta bayyana dalilin da ya sa ta dauki wannan mataki ba, ana ganin hakan a matsayin wani bangare na kokarin sake fasalta tsarin shugabanci a bangaren ilimin jihar.
Kebbi ta maida ilimi kyauta ga ƴan jihar
A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta ayyana ilimi kyauta tare da ƙara yawan kuɗin da ake warewa wajen ciyar da ɗaliban makarantun sakandare.
Gwamnan jihar, Nasir Idris ne ya bayyana hakan, ya ƙara da cewa an yi karin daga Naira miliyan 200 zuwa Naira miliyan 350 domin dafa wa daliban abinci duk wata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng