Asadussunah Ya Bukaci Izalar Jos da Kaduna Su Mayar da Wukar Yaki da Juna
- Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya ce mafi yawan mabiya Izala ba sa son rikicin da ake tsakanin malaman Jos da Kaduna
- A karkashin haka, Asadussunnah ya bukaci malaman Izala su daina kiran juna da sunaye kala kala kamar yadda Alkur’ani ya haramta
- Malamin ya gargadi shugabannin Izala da su mayar da hankali kan matsalolin da suka fi addabar al’umma a kan kokarin kare kansu
- Legit ta tattauna da wani limamin masallacin Izala inda ya bayyana ra'ayinsa kan rikicin da ya bullo a kungiyar.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah, ya yi kira ga malaman Izala da ke Jos da Kaduna su daina rikici a tsakaninsu.
Malamin ya ce mafi akasarin mabiya Izala ba sa son rikicin, amma kawai ba su da ikon fitowa su fadi gaskiya a fili ne.

Kara karanta wannan
'Ku bar sukar Tinubu': Malamin Musulunci kan tsadar rayuwa, ya kawo mafita ga yan kasa

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da malamin ya yi ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana haka ne yayin da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin bangaren Sheikh Sani Yahaya Jingir da ke Jos da Sheikh Abdullahi Bala Lau da ke bangaren Kaduna.
Kira ga 'yan Izala su sasanta juna
Sheikh Asadussunnah ya bayyana cewa ba haduwar Izala ake magana ba a halin yanzu, sai dai yadda ‘yan Izala daga bangarori za su yarda da juna su yi aiki tare.
A cewarsa, tun da malaman Izala suka fito fili suna yi wa juna raddi, dole ne a fito fili a yi musu nasiha da gaskiya.
Malamin ya kara da cewa su da suke cewa su ne daliban Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, sun san cewa ba haka yake ba, domin shi bai damu da kare kansa ba, sai dai kare addinin Musulunci.
Magana kan kiran juna da sunaye
Sheikh Asadussunnah ya tunatar da malaman Izala cewa Alkur’ani ya haramta wa Musulmi kiran juna da sunan banza.
Ya ce bai dace manyan malaman addini su rika rikici ba, domin hakan bai dace da matsayinsu a addini ba.
Malamin ya ce lokaci ya yi da za a daina sukar juna, a maimakon haka, malamai su mayar da hankali kan ilmantar da al’umma da kuma dakile bidi’a kamar yadda aka kafa Izala don hakan.
Bukatar fuskantar matsalolin kasa
Sheikh Asadussunnah ya gargadi shugabannin Izala da su duba halin da kasa ke ciki a maimakon su rika jefa kansu cikin rikici maras amfani.
Ya ce yana fargabar kar wannan rashin jituwa ta haifar da gaba mai tsanani fiye da kalaman baki, ta kai ga ana fada da juna.
A cewarsa, a halin da ake ciki, ya kamata malaman Izala su mayar da hankali wajen fahimtar da mutane game da matsalolin da ke addabar al’umma maimakon su karkata ga rikici tsakaninsu.
Malamin ya kammala da yin kira ga malamai da su rungumi hakuri, su zauna lafiya tare da juna, domin tabbatar da ci gaban addini da kuma zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Legit ta tattauna da limamin Izala
Wani limami a masallacin Izala, Ustaz Usman Abdullahi ya zantawa Legit cewa ba sa jin dadin rikicin sam.
"Bai kamata a rika samun haka daga gare su ba. Su ne jagorori da ya kamata su rika yi wa mutane fada.
'Ya kamata su yi amfani da abin da suke fada wa mutane wajen wa'azi su sasanta tsakaninsu."
- Usman Abdullahi
Limamin Abuja ya yi kira ga malamai
A wani rahoton, kun ji cewa limamin masallacin kasa na Abuja ya yi nasiha ga malamai kan nisantar sukar juna.
Sheikh Abdulkadir Salman Sholagberu ya ce sukar juna ba shi da wani amfani ga addini sai dai ma ya kara rage darajar Musulunci.
Asali: Legit.ng