"Najeriya Ta Yi Rashi," Tinubu Ya Kaɗu da Allah Ya yi wa Fitaccen Malamin Musulunci Rasuwa

"Najeriya Ta Yi Rashi," Tinubu Ya Kaɗu da Allah Ya yi wa Fitaccen Malamin Musulunci Rasuwa

  • Mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar shahararren malamin musulunci, Sheikh Modibbo Ibrahim Daware
  • A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa ya fitar, Tinubu ya ce wannan rashin ba iyalan mamacin kaɗai ya shafa ba, har da ƙasa baki ɗaya
  • Sheikh Daware, fitaccen malamin ɗarikar Tijjaniya a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas ya rasu ne ranar Juma'a bayan fama da jinya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar jimami kan rasuwar Sheikh Modibbo Ibrahim Daware, fitaccen malamin addinin Islama a jihar Adamawa.

Sheikh Daware jagora ne mai daraja a darikar Tijjaniyya, wanda ya kwashe rayuwarsa yana koyar da ilimi, kira zuwa ga shiriyar Allah da kuma gyara ɗabi'un mutane da dama.

Kara karanta wannan

Duniya ba tabbas: An sake rashin babban malamin Musulunci a Najeriya, Atiku ya jajanta

Sheikh Daware da Bola Tinubu.
Bola TInubu ya yi jimamin rasuwar babban malamin musulunci a Adamawa, Sheikh Modibbo Ibrahim Daware Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin soshiyal midiya, Dada Olusegun ne ya wallafa sakon ta'aziyyar Bola Tinubu a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya kaɗu da rasuwar Sheikh Daware

A cikin sanarwar mai ɗauke da sa hannun kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, Tinubu ya yi alhini tare da miƙa sakon ta'aziyya bisa rasuwar malamin.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Sheikh Modibbo Ibrahim Daware ya rasu ne da safiyar ranar Juma’a da ta gabata bayan fama da jinya ta tsawon lokaci.

Shugaba Tinubu ya yaba da tawali’u, tsoron Allah da kuma sadaukarwar Sheikh Daware wajen neman ilimi.

Rasuwar malamin babban rashi ne a ƙasa

Ya bayyana rasuwar babban malamin a matsayin babban rashi, ba ga iyalansa da al’ummarsa kadai ba, har ma ga kasa baki daya.

"Ina mika ta'aziyyata ga gwamnatin jihar Adamawa, iyalan marigayin da mabiyansa. Allah ya ji kan sa da rahama kuma ya lulluɓe kabarinsa da ni'ima.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya yi wa El Rufai wankin babban bargo, ya fadi wani sirrinsa

"Rayuwar marigayi Sheikh Daware za ta ci gaba da zaburar da mu, da tunatar da mu muhimmancin addini, ilimi da kuma hidima ga al’umma ba tare da son kai ba," in ji Shugaba Tinubu.

Atiku ya miƙa sakon ta'aziyya a Adamawa

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi ta'aziyyar rasuwar Sheikh Modibbo Ibrahim Daware.

Wazirin Adamawa ya ce malamin, wanda tsohon shugaban ƙungiyar Fityanul Islam ta Adamawa ne, ya kasance mutumin da Allah ya yi wa baiwa da sanin ilimin fikhu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel