Ana Kuka da Tsadar Fetur, Gwamnatin Tinubu Ta Ja Kunnen 'Yan Najeriya kan Cire Tallafi

Ana Kuka da Tsadar Fetur, Gwamnatin Tinubu Ta Ja Kunnen 'Yan Najeriya kan Cire Tallafi

  • An buƙaci ƴan Najeriya da su daina sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi
  • Hadimar Shugaba Tinubu, Khadijat Omotayo ce ta yi wannan kiran a wajen wani taro a birnin Jos na jihar Plateau
  • Ta bayyana cewa shugaban ƙasan ya ƙara yawan kuɗaɗen da ake ba jihohi sakamakon cire tallafin man fetur ɗin da aka yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Mataimakiya ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan harkokin mazaɓu, Khadijat Omotayo, ta yi magana kan cire tallafin man fetur.

Khadijat Omotayo ta buƙaci ƴan Najeriya da su daina sukar Shugaba Tinubu kan cire tallafin man fetur.

An bukaci a daina sukar Tinubu kan cire tallafi
An kare Tinubu kan cire tallafin man fetur Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Hadimar shugaban ƙasan ta yi wannan kiran ne a ranar Asabar a garin Jos, babban birnin jihar Plateau, yayin wani taro, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya yi wa El Rufai wankin babban bargo, ya fadi wani sirrinsa

An kare Tinubu kan cire tallafin fetur

Taron ya haɗa shugabannin ƙungiyoyi daban-daban, kamar mata ƴan kasuwa, matasa, shugabannin ƙwadago, manoma, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati, ɗalibai da sauransu.

A cewarta, Shugaba Tinubu na da ƙudirin aiwatar da shirye-shirye waɗanda za su inganta rayuwar duk ƴan Najeriya.

Ta jaddada cewa kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin man fetur an raba su ga dukkan jihohi, kuma shugaban ƙasa ya ƙara albashin ma’aikata tare da alƙawarin yin sabon ƙarin albashi a nan gaba.

Shugaba Tinubu ya samu yabo

Khadijat Omotayo ta yabawa Tinubu wajen haɗa kan ƴan ƙasa gaba ɗaya, inda ta ce zuwanta Plateau, wacce PDP ke mulki, alama ce da ke nuna cewa Tinubu na son yin aiki tare da duk ƴan Najeriya ba tare da nuna bambanci ba.

Haka kuma, ta jinjinawa gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang, saboda ƙoƙarinsa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da haɗa kan mutanen jihar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Wike ya ba 'yan Najeriya mafita kan manufofin gwamnatin Tinubu

"A wannan lokaci, bai kamata mu ci gaba da sukar shugaban ƙasa ba, wanda burinsa shi ne tabbatar da cewa romon dimokuraɗiyya ya isa a dukkanin jihohi."
"Idan da shugaban ƙasa yana son yin siyasa ta son zuciya, da bai bari na zo jihar Plateau ba, kasancewar PDP ce ke mulki a nan."
"Amma na zo a madadinsa domin yana son haɗa kowa da kowa. Lokacin zaɓe, mun fafata kuma mun yi nasara. Bayan zaɓe, dole ne mu haɗa dukkan al’ummar Najeriya."
"Eh, shugaban ƙasa ya cire tallafin man fetur, amma kuɗaɗen da aka samu sakamakon hakan an raba su ga dukkan jihohi."
"Game da ƙarin albashi, yaushe ne lokaci na ƙarshe da wani shugaban ƙasa ya ƙara albashin ma’aikata? Don haka, ina ganin shugaban ƙasa ya cancanci godiya daga gare mu."
"Har yanzu bai cika shekara ɗaya a ofis ba, amma ya riga ya ƙara albashin ma’aikata, kuma ya ce wannan ba zai zama ƙarin albashi na ƙarshe ba a mulkinsa."

- Khadijat Omotayo

Gwamnatin Tinubu za ta raba tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu za ta raba tallafi ga ƴan Najeriya.

Gwamnatin ta hannun ma'aikatar mata da ci gaban al'umma za ta raba tallafin ne ga mata har miliyan 4.5 a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng