Yan Sanda Sun Yi Bajinta, Sun Ceto Fitaccen Basarake bayan Shafe Kwanaki a Wurin Miyagu

Yan Sanda Sun Yi Bajinta, Sun Ceto Fitaccen Basarake bayan Shafe Kwanaki a Wurin Miyagu

  • Jami’an ‘yan sanda a Edo sun yi bajinta bayan nasarar ceto wani basarake da aka sace a jihar tun farkon watan Fabrairun nan
  • Yan sanda sun ceci Onogie na Udo-Eguare, wanda aka sace a ranar 3 ga Fabrairun 2025, bayan kwana hudu a hannun miyagu
  • Kwamishinan ‘yan sanda na Edo, Betty Otimenyin, ta jagoranci aikin ceton, tare da hadin gwiwar gwamnati da jami’an tsaro na sa-kai
  • ‘Yan sanda sun yaba da goyon bayan Gwamna Monday Okpebholo, suna tabbatar da cewa suna ci gaba da jajircewa wajen yaki da ta'adi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Benin City, Edo - Jami’an ‘yan sanda a Jihar Edo, kudu maso Kudancin Najeriya, sun ceto wani basarake da aka yi garkuwa da shi.

Yan sanda suka ce sun ceto Onogie na Udo-Eguare, basaraken gargajiya da aka sace a ranar 3 ga Fabrairun 2025.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mutum 9 da ake zargi da hannu a kisan ɗan majalisa

Yan sanda sun ceto basarake daga masu garkuwa da mutane
Rundunar yan sanda a Edo ta yi nasarar ceto basarake bayan sace shi. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan sanda sun magantu kan ceto basarake

Kakakin rundunar, Moses Yamu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a Benin, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an ceto shi ne a ranar Juma’a 7 ga watan Janairun 2025 da misalin karfe 6:00 na yamma.

Ya bayyana cewa nasarar ta samu ne sakamakon kokarin ‘yan sanda tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Edo da yan Banga da mafarauta da mazauna yankin.

Jami'an yan sanda sun mika godiya ga al'umma

Yamu, babban jami’in ‘yan sanda, ya ce Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Betty Otimenyin, ta yi alkawarin ceto shi, kuma tawagarta ta yi aiki ba dare ba rana.

Ya ce rundunar ta gode wa Gwamnatin Jihar Edo, tare da danganta nasarar da gudunmawar da Gwamna Monday Okpebholo ya bayar ta fuskar kayan aiki, Premium Times ta ruwaito.

“Muna kuma godiya ga yan banga, mafarauta da sauran mazauna jihar da suka ba da gudunmawa. ‘Yan sanda na ci gaba da jajircewa wajen yaki da laifi."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki masallaci, sun sace limami da masallata

- Cewar Mista Yamu

Yadda yan bindiga suka sace basarake

A baya, kun ji cewa ana zargin wasu miyagun yan bindiga sun tare basarake a kan titi, sun yi awon gaba da shi bayan halaka ɗan acaɓar da ya ɗauko shi a jihar Edo.

Bayan sace Mai Martaba Friday Ehizojie, an kuma yi garkuwa da wasu mutum biyar, amma daya daga cikinsu ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane.

Kwamishinar ‘yan sanda ta ba da umarnin tura jami’an tsaro domin tabbatar da kubutar da wadanda aka sace da kuma kamo wadanda suka aikata laifin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.