'Na So Zama Soja': Gwamnan PDP Ya Fadi Burinsa yayin Jimamin Mutuwar Yayansa
- Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya bayyana cewa yana da burin shiga soja, amma hakan bai samu ba saboda wasu dalilai
- Makinde ya bayyana cewa marigayi babban yayansa, Sunday Olufunmilayo Makinde, ya taka rawa wajen kirkirar wannan buri nasa
- Duk da cewa burin shiga soja bai cika ba, darussan da ya koya daga yayansa sun taimaka masa wajen jagorancin jihar Oyo a yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ibadan, Oyo - Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya bayyana burin da yake da shi a bayan kafin shiga siyasa.
Seyi Makinde ya ce yana da burin shiga soja amma bai yi nasara ba saboda wasu dalilai masu karfi.

Asali: Facebook
Gwamna Makinde ya fadi burin da ya so a baya
BusinessDay ta ce mutane da dama sun sanshi a matsayin ɗan siyasa da ɗan kasuwa, ƙalilan ne suka san da wannan burin nasa da bai cika ba.

Kara karanta wannan
Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makinde ya bayyana cewa hakan ya samu tasiri ne daga babban yayansa, Injiniya Sunday Olufunmilayo Makinde.
A yayin bikin girmamawa ga yayansa bayan rasuwarsa, Gwamna Makinde ya bayyana irin kusancin da suke da shi.
Ya tuna yadda a shekarar 1982, suna kwanciya a gadon mahaifinsu wanda ya kara kusanta su, ya samar da alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu.
Gwamnan ya ce Sunday Makinde ba kawai babba bane, amma abin koyi ne, nasarorinsa sun fadada tunaninsa, suka kuma zaburar da shi ya kammala digirinsa na farko.
Amma kafin ya yi yunkurin shiga soja wannan hanya ba ta yi masa kyau ba saboda abin ya zo ya zama.
Gwamna ya yaba wa halayen marigayi yayansa
Duk da haka, dabi’un da Sunday ya dasa masa na naci, gaskiya, da shugabanci nagari—har yanzu suna tare da shi, inda ya jaddada rawar da yayansa ya taka wajen haɗa iyalinsu wuri ɗaya.

Kara karanta wannan
'Na bambanta da su': Buhari ya fadi halin da abokansa na yarinta da karatu ke ciki
Ko da yake rashin yana da yawa, Gwamna Makinde ya sami kwanciyar hankali da sanin cewa Sunday Makinde ya yi rayuwa mai amfani da cikar muradi.
“Za ka ci gaba da rayuwa a zuciyata, kuma zan riƙe ƙaunar ka har abada."
- Seyi Makinde
Ko da yake burinsa na saka kayan soja bai cika ba, a yanzu Seyi Makinde yana yi wa Jihar Oyo hidima ta wata hanya.
Gwamna Makinde ya biya mafi ƙarancin albashi
Kun ji cewa ma'aikatan jihar Oyo sun cika da murna bayan an fara biyansu sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 a watan Janairun 2025.
Gwamnatin jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta cika alƙawarin da ta dauƙa na fara biyan ma'aikatan sabon mafi ƙarancin albashin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng