Wani Abin Fashewa Ya Tarwatse a Matatar Man Feturin Najeriya? NNPCL Ya Yi Bayani

Wani Abin Fashewa Ya Tarwatse a Matatar Man Feturin Najeriya? NNPCL Ya Yi Bayani

  • Kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya musanta raɗe-raɗin da ake cewa wani abu ya fashe a matatar man gwamnati da ke Warri
  • A wata sanarwa da mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye ya fitar ranar Juma'a, ya ce babu wata fashewa da ta auku
  • Mista Soneye ya tabbatar da cewa aklna gyara a ɓangare ɗaya na matatar Warri amma nan ba da jimawa ba za a kammala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta - Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa babu wani abin fashewa da ya tarwatse a matatar mai ta Warri watau WRPC.

Jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Olufemi Soneye, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a da daddare.

Matatar Warri.
NNPCL ya karyata rahoton da ake cewa wani abu ya fashe a matatar man gwamnatin Najeriya da ke Warri Hoto: @NNPCLimited
Asali: Twitter

Kamfanin NNPCL ya wallafa wannan sanarwa ɗauke da sa hannun Soneye a shafinsa na manhajar X jiya Juma'a, 7 ga watan Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan

"Ka yi zamanka a PDP," Sanata ya gargaɗi gwamnan da ake raɗe raɗin zai koma APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin NNPCL, Mista Oƙufemi Soneye ya karyata rahotannin da ake yaɗawa cewa an samu fashewa a matatar man Warri.

"Babu wani abin da ya fashe"- NNPC

Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa duk wani rahoto da ke cewa an samu fashewa a matatar karya ne.

A cewar Soneye:

"NNPCL yana tabbatar da cewa babu wani abin fashewa da ya tashi a matatar man gwamnati da ke Warri watau WRPC. Duk wani rahoto da ya ce haka, ba gaskiya ba ne."

Ya kuma ƙara cewa a ranar 25 ga Janairu, an dakatar da ayyukan ɓangaren farko na matatar domin gudanar da gyare-gyaren gaggawa a wasu kayayyakin aiki.

Dalilin gyaran da ake yi a matatar Warri

Ya ce aikin gyaran yana da muhimmanci domin tabbatar da samar da isassun kayayyaki kamar dizel da da kalanzir masu inganci.

Mai magana da yawun NNPCL ya ce gyaran yana tafiya cikin tsari, kuma za a koma aiki a ɓangaren cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Kara karanta wannan

"Me suke shiryawa?": Ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa Sanata Binani ta bar baya da ƙura

"Duk da gyare-gyaren da ake yi, har yanzu ana loda man dizil a matsakaitan motoci takwas a kowace rana, kuma akwai isasshen wadatar danyen mai domin ci gaba da lodin kaya," in ji shi.

A ranar 30 ga Disamba, NNPCL ya sanar da cewa an gyara matatar Warri, kuma ta fara samar da wasu kayayyaki.

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa matatar tana aikin kashi 60 cikin 100 na karfinta, amma har yanzu ba ta fara samar da man fetur (PMS) ba.

Aikin da matatar man Warri ke yi

A yanzu, matatar Warri tana mayar da hankali ne wajen samar da kayayyaki kamar kalanzir da man dizel.

Mista Soneye ya ce NNPCL zai ci gaba da ƙoƙarin wadatar da mai a Najeriya, tare da bukatar jama’a da su yi hakuri yayin da ake kammala gyaran.

Farashin fetur zai kara karyewa a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa ƴan kasuwa sun yi hasashen cewa nan gaba farashin man fetur zai sake karyewa a Najeriya.

Kara karanta wannan

A hukumance, jam'iyyar APC ta samu ƙarin sanata 1 a Majalisar Dattawan Najeriya

Ƙungiyar ƴan kasuwar mai watau PETROAN ta hango wannan sauƙi da ke tafe, tana mai cewa matatun mai sun fara aiki gadan-gadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262