An Shiga Tashin Hankali a Kano, Gobara Ta Kashe Dabbobi 78, Ta Lalata Kayan Abinci

An Shiga Tashin Hankali a Kano, Gobara Ta Kashe Dabbobi 78, Ta Lalata Kayan Abinci

  • Wata mummunar gobara ta kashe shanu, tumaki, awaki da kaji 78 a kauyen Danzago, karamar hukumar Dambatta a jihar Kano
  • Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta sanar da cewa ta ceto shanu hudu, tumaki biyu da rumbuna biyu daga wannan gobarar
  • An ce wani jami'in hukumar kashe gobara ya ji rauni a kafa yayin kokarin kashe gobarar amma an tabbatar da cewa babu asarar rai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Akalla shanu, tumaki, awaki da kaji 78 sun kone a wata gobara da ta tashi a kauyen Danzago, karamar hukumar Dambatta a jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba a gidan Ado Yubai.

Hukumar kashe gobara ta Kano ta magantu da gobara ta tashi a gidan wani mutumi
Gobara ta tashi a gidan gonar wani mutumi a Kano, dabbobi 78 sun mutu. Hoto: @Fedfireng
Asali: UGC

Saminu ya bayyana cewa ofishinsu a Dambatta ya samu kiran gaggawa daga Abdurashid Sha’aibu wanda ya sanar da faruwar gobarar, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobarar ta tashi a gidan wani mutumi a Kano

Kakakin hukumar kashe gobarar ya ce:

"Mutanenmu daga ofishin Dambatta sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka tarar da gidan Ado Yubai yana ci da wuta."

Saminu Abdullahi ya ce gidan yana da fadin ƙafa 200 x 200, yana da sassa tara, ɗakuna 17 da wurin ajiyar kayayyaki guda daya.

"Gobara ta kashe shanu biyu, tumaki 36, awaki 17 da kaji 10, har da rumbunan ajiya 19," inji Saminu.

Gobara: Wuta ta kashe dabbobi da kona abinci

Kakakin hukumar ya ci gaba da cewa:

"Da taimakon Allah, an ceto shanu hudu da tumaki biyu, tare da rumbun ajiyar kayan abinci biyu da wasu kayan amfani."

Sai dai ya ce gobarar ta kashe dabbobi da suka hada da shanu, tumaki, awaki da kaji kusan guda 78, sannan ta lalata rumbunan abinci.

Haka zalika, Saminu ya ce gobarar ta bazu zuwa gidan Ibrahim Mai Gariyo, inda rumfa ɗaya da tumaki takwas da awaki uku suka kone.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a Kano, ta jawo gagarumar asara

Abdullahi ya ce wani jami’insu ya samu raunin wuta a ƙafa yayin kashe gobarar, amma babu wanda ya rasa ransa.

Abba ya raba awakin N2.3bn a jihar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Yusuf ya kare shirin raba awaki ga mata, yana mai cewa naman awaki na da amfani ga lafiya da tattalin arziki.

A cikin shirin, mata 7,158 ne suka amfana da tallafin awaki a kananan hukumomi 44 na jihar Kano, domin rage talauci da sama masu hanyar samun kudi.

Gwamnan ya ce Bankin Musulunci ne ya tallafa wa shirin, inda aka kashe naira biliyan 2.3 wajen saye da rarraba awakin ga mata a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.