Tinubu Ya Runtuma Kora a Jami'o'in Tarayya, Ya Tsige Shugabar UniAbuja, Aisha Maikudi
- Bola Tinubu ya tsige Farfesa Aisha Maikudi daga shugabancin jami’ar Abuja, ya maye gurbinta da Lar Patricia Manko a matsayin mukaddashiya
- Shugaba Tinubu ya sauya shugabancin jami’o’i da dama, ciki har da UNN, inda aka nada Farfesa Oguejiofu T. Ujam a matsayin shugaba
- Sauye-sauyen sun hada da nada sababbin Pro-Chancellors a jami’o’in tarayya, ciki har da Sanata Sani Stores da Sanata Lanre Tejuoso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke Farfesa Aisha Maikudi daga mukaminta na shugabar jami’ar Abuja (UniAbuja).
Bola Tinubu ya sanar da sauke Maikudi ne bayan sa’o’i kadan da ta jagoranci bikin yi wa sababbin dalibai maraba da shiga jami’ar.

Asali: Twitter
UniAbuja: Bola Tinubu ya tsige Aisha Maikudi
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa an yi ce-ce-ku-ce kan nadin Aisha Maikudi, inda wasu malaman jami’ar suka ce ba ta cancanci rike mukamin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya nada Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin mukaddashiyar shugabar jami’ar na tsawon watanni shida, kuma ba za ta nemi zama cikakkiyar VC din ba.
Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da gwamnatin tarayya ta sauya sunan jami'ar Abuja zuwa jami'ar Yakubu Gowon.
Shugaba Tinubu ya tsige shugaban jami'ar UNN
Shugaban kasa ya kuma tsige Farfesa Polycarp Emeka Chigbu daga mukaminsa na mukaddashin shugaban jami’ar Najeriya, Nsukka (UNN), inji Premium Times.
Dama dai an tsara Farfesa Chigbu zai kammala wa'adinsa a ranar 14 ga Fabrairu, amma Tinubu ya nada Farfesa Oguejiofu T. Ujam a matsayin sabon mukaddashin shugaban jami’ar.
Sabon mukaddashin shugaban jami’ar UNN zai yi watanni shida a ofis, kuma ba zai nemi zama cikakken shugaban jami'ar ba.
Tinubu ya yi garambawul a jami'o'in tarayya
A jami'ar UNN, Tinubu ya sauya shugabancin majalisar jami’ar, inda aka sauya Janar Ike Nwachukwu zuwa shugaban majalisar jami'ar Uyo.

Kara karanta wannan
"Waye sakataren PDP?" Barau Jibrin ya zaƙalƙale da hatsaniya ta ɓarke a Majalisar Dattawa
Tinubu ya nada Injiniya Olubunmi Kayode Ojo a matsayin sabon shugaban majalisar jami'ar UNN. Ojo ya rike wannan mukami a jami’o’in Lokoja da Oye-Ekiti.
Farfesa Zubairu Tajo Abdullahi, wanda ke matsayin shugaban majalisar jami'ar Uyo, yanzu ya maye gurbin Ojo a Jami’ar Lokoja.
Har ila yau, Sanata Sani Stores ya zama sabon shugaban majalisar jami'ar Alvan Ikoku, inda ya maye gurbin Sanata Joy Emordi.
Barista Olugbenga Kukoyi, mamba na kwamitin jami’ar UNN, ya zama sabon shugaban majalisar jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka.
Sanata Lanre Tejuoso, shugaban majalisar jami’ar Noma ta Makurdi, ya koma Jami’ar Yakubu Gowon, inda Sanata Joy Emordi ta maye gurbinsa a Makurdi.
Aisha Maikudi ta zama shugabar jami'ar Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Farfesa Aisha Maikudi ce aka naɗa sabuwar shugabar Jami’ar Abuja (UniAbuja) da ke birnin tarayya, Abuja.
A ranar Talata, 31 ga Disamba, 2024, majalisar gudanarwar jami’ar ta amince da naɗin Aisha Maikudi a matsayin sabuwar shugaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng