Yaro 'Dan Firamare Ya Je Makaranta da Bindiga Yana Barazanar Harbe Dalibai
- Rundunar 'yan sanda a jihar Akwa Ibom ta kama yaro ɗan shekara 13 da bindiga a makaranta yana tsoratar da ‘yan ajinsu
- Biyo bayan lamarin, 'yan sanda sun kama mahaifin yaron bayan ya bayyana cewa ya samo bindigar daga ɗakin uban nasa a gida
- Rahotanni sun nuna cewa a yanzu haka rundunar ‘yan sandan jihar na cigaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Akwa Ibom - Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta cafke wani yaro ɗan shekara 13 mai suna Samuel Sunday dalibin makarantar firamare ta St. Paul, Ikot Ibiok da ke Eket.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Samuel Sunday ne bayan an same shi da bindiga a makaranta yana tsoratar da abokan karatunsa.

Asali: Facebook
Jaridar Tribune ta wallafa cewa rundunar ta kama yaron tare da mahaifinsa bayan da ya bayyana cewa ya samo bindigar daga cikin ɗakin mahaifinsa tun watan Nuwamba 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’ar hulɗa da jama’a ta ‘yan sandan jihar, DSP Timfon John ta bayyana cewa an kama yaron ne bayan samun ƙorafi daga shugabannin makarantar.
Hukumar makaratar da mika korafi ne bayan an zargi yaron da amfani da bindigar yana barazana ga sauran ɗalibai.
Yadda aka kama mahaifin yaro mai bindiga
DSP Timfon John ta bayyana cewa bayan samun rahoton gaggawa daga makarantar, jami’an tsaro sun gaggauta kama yaron tare da kwace bindigar.
Aminiya ta rahoto DSP Timfon John tana cewa:
"A ranar Talata 30 ga Janairu, 2025 da misalin ƙarfe 8 na safe, rundunar ‘yan sanda ta samu bayani cewa wani yaro mai suna Samuel Sunday yana rike da bindiga a makaranta.
"Lamarin ya faru ne a makarantar firamare ta St. Paul kuma yana barazanar harbin abokan karatunsa."
"Jami’an mu sun gaggauta zuwa wurin suka kama shi tare da kwace bindigar kuma an kama mahaifinsa."
Me ya sa yaron ya dauki bindiga?
Har yanzu ba a bayyana dalilin da yasa yaron ya ɗauki bindiga zuwa makaranta ba, amma binciken farko na nuna cewa ba shi ne karo na farko da yake riƙe da makamin ba.
Rundunar ‘yan sanda ta jaddada cewa za ta binciki lamarin sosai domin tabbatar da cewa an dauki matakan da suka dace don hana irin haka faruwa a gaba.
An kama masu satar yara a Akwa Ibom
Haka zalika, ‘yan sanda sun kuma kama wasu mata biyu Roseline Maurice da Eno Udoka bisa zargin haɗa baki wajen satar wani yaro a garin Obong Itam.
DSP Timfon John ta bayyana cewa mutanen biyu sun sace yaron ne sannan suka sayar da shi ga wani mai sayen yara a jihar Cross River kan kuɗi N200,000.
Bayan samun kuɗin, sun yi amfani da su wajen sayen kayan gida kamar firji, talabijin da fanka da sauransu.
Badaru ya yi magana kan 'yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya ce sun shirya tsafa domin magance matsalar tsaro.
Badaru ya bayyana haka a wani taro inda ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya matsa musu lamba kan magance matsalar 'yan bindiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng