Sheikh Guruntum: Muhimmancin Sulhu da Juna kafin Watan Ramadan

Sheikh Guruntum: Muhimmancin Sulhu da Juna kafin Watan Ramadan

  • Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya ce yana da muhimmanci Musulmi masu gaba da juna su yi sulhu kafin shigowar watan Ramadan
  • Malamin ya bayyana cewa husuma da gaba suna hana karɓar azumi, don haka yana da kyau a daidaita sabani kafin watan azumi ya kama
  • Sheikh Guruntum ya jaddada muhimmancin ciyarwa a Ramadan, yana mai ishara da cewa ya kamata kowa ya yi iya kokarinsa wajen ciyarwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum, ya yi kira ga Musulmi da su yi sulhu da juna kafin shigowar watan Ramadan.

Malamin ya bayyana cewa duk wanda ke da husuma da wani Musulmi, to ya tabbata ya daidaita tsakaninsu, domin hakan yana da matukar muhimmanci wajen karɓar ibadar azumi.

Kara karanta wannan

Dan Bello ya magance matsalar ruwa a kauyukan Katsina, ya jefa kalubale ga Buhari

Guruntum
Sheikh Guruntum ya yi nasiha ga Musulmi a kan azumin Ramadan. Hoto: Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
Asali: Facebook

Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, Sheikh Guruntum ya jaddada muhimmancin ciyarwa a watan Ramadan, yana mai cewa hakan yana daga cikin manyan ayyukan lada da suke da daraja mai girma a wajen Allah.

Muhimmancin sulhu kafin zuwan Ramadan

A cikin wa’azinsa, Sheikh Guruntum ya ce husuma da gaba suna hana karɓar azumi, wanda hakan zai iya tasiri ga azumin da mutum zai yi a watan Ramadan.

"Duk wanda ke da sabani da wani Musulmi, ya tabbatar da cewa sun daidaita kafin shigowar Ramadan.
"Idan ka nemi sulhu kuma mutum ya ƙi, to kai ka sauke nauyin da ke kanka,"

- Sheikh Ahmad Guruntum

Sheikh Yusuf Guruntum ya ce wajibi ne Musulmi su rungumi juna da hakuri, su guji husuma da rikici.

Malamin ya ce kar mutum ya bari Ramadan ya kama yana gaba da wani Musulmi. Wannan yana hana karɓar ibada wanda hakan zai iya hana samun albarkar watan.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya fara gyara hanyar Saminaka da ta hada jihohin Arewa

Ana ganin cewa sulhu da juna ba kawai yana taimakawa wajen samun lada ba ne, har ma yana kara karfafa zumunci da kawar da husuma a cikin al’umma.

Malamin ya koka da cewa wani lokaci ana iya samun gaba tsakanin 'yan uwa wanda ke shafar iyalansu wanda hakan bai dace ba.

Muhimmancin ciyarwa a watan Ramadan

Sheikh Guruntum ya bayyana cewa ciyarwa na da matukar muhimmanci a cikin watan Ramadan, kuma hakan yana daga cikin manyan ayyukan lada.

Malamin ya kara da cewa da masu hali za su san irin ladan da ke cikin ciyarwa, da sun yi ƙoƙarin ba da sadaka da ciyar da mutane sosai a cikin Ramadan.

Yadda magabata ke ciyar da al'umma

Sheikh Saleh Al-Munajjid ya kawo misalai daga rayuwar magabata, inda ya ce suna ciyar da mutane fiye da yadda ake zato.

Malamin ya wallafa a shafinsa cewa cewa wani daga cikin magabata na kwarai ya ce:

Kara karanta wannan

Sheikh Guruntum ya tsage gaskiya ga malamai masu cudanya da 'yan siyasa

"Gara in gayyaci mutane goma in ba su abinci fiye da in ‘yantar da bayi goma daga zuriyar Annabi Isma’il."

Sheikh Guruntum ya yi nasiha ga malamai

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi nasiha ga malamai ma su cudanya da 'yan siyasa.

Sheikh Gurutum ya bayyana illolin da malamai za su iya fuskanta idan suka ci gaba da mu'amala maras iyaka da 'yan siyasar kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng