Duk da Korafe Korafe kan Masarautu, Gwamna Ya Nada Dan Uwan Nuhu Ribadu Sarauta

Duk da Korafe Korafe kan Masarautu, Gwamna Ya Nada Dan Uwan Nuhu Ribadu Sarauta

  • Gwamna Ahmadu Fintiri ya nada Alhaji Muhammadu Sani Ahmadu Ribadu a matsayin Sarkin Fufore, sabon masarautar da aka kafa a jihar Adamawa
  • Gwamna Fintiri ya ce kafa masarautar zai taimaka wajen warware rikice-rikice, inganta shugabanci na gari, da karfafa dimokuradiyya a yankin
  • Sabon Sarkin ya gode wa gwamnati inda ya yi alkawarin shugabanci na adalci tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Fufore
  • Wannan nadin sarauta da sauran sababbin masarautu bakwai a jihar ya jawo maganganu kan karfin ikon Lamidon Adamawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Yola, Adamawa - Dan uwan Mai ba shugaban kasa shawara kan lamarin tsaro, Nuhu Rbadu ya zama sarki a jihar Adamawa.

Gwamna Ahmadu Fintiri ya nada Alhaji Muhammadu Ahmadu Ribadu, ɗan’uwan Ribadu a matsayin Sarkin Fufore a Jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Tinubu ya bayyana babban abin da ya saka a gaba a Najeriya

Dan uwan Nuhu Ribadu ya zama sarki a jihar Adamawa
Gwamna Ahmadu Fintiri ya ba dan uwan Nuhu Ribadu sandar sarauta a matsayin Sarkin Fufore. Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri.
Asali: Facebook

Gwamna Fintiri ya ba Ribadu sandar sarauta

Gwamnan ya bayyana haka a shafinsa na Facebook inda ya ce an samar da dokar nadin sarakuna ta Adamawa ta 2024 domin bai wa masarautu cikakken matsayi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, da kansa ya miƙa masa sandar mulki, yana mai cewa kafa masarautar wata babbar manufa ce don inganta sulhu da haɗin kai.

Fintiri ya yi imani cewa kafa masarautar zai taimaka wajen haɗa kan jama’a da kuma samar da tsari na mulki mai isa ga yankunan da ke nesa.

Fintiri ya fadi tsarin zaben Ribadu sarauta

Ya bayyana cewa nadin Ribadu ya dogara ne da cancanta, inda ya bukace shi da ya yi shugabanci mai hikima da kuma karfafa tsaro ta hanyar tattara bayanai.

"Ina mai farin cikin bayyana cewa, a yau na mika sandar mulki ga Sarkin Fufore na farko, Mai Martaba Alhaji Sani Ahmadu Ribadu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gana da Aminu Ado Bayero, ya ba shi tabbacin kawo karshen matsaloli a Kano

"Na kuma gargade shi da ya jagoranci mutanensa da adalci, hadin kai, da ci gaban masarautar."

- Ahmadu Umaru Fintiri

Jawabin godiya daga Sarki Ribadu

A jawabin karɓar sarautarsa, sabon sarki ya gode wa gwamna bisa amincewa da shi, yana mai alƙawarin zama shugaba na adalci ga kowa da kowa.

“Ina tabbatar muku da cewa, a ƙarƙashin jagorancina, kowa zai sami adalci ba tare da tsoro ko son zuciya ba.”

- Alhaji Sani Ahmadu Ribadu

Sabon sarkin ya kuma roki goyon bayan jama’a domin sauke nauyin da ke wuyansa tare da inganta zaman lafiya da ci gaban masarautar.

Taron nadin ya samu halartar manyan sarakuna daga ciki da wajen jihar Adamawa, da tsofaffi da sababbin jami’an gwamnati, da ‘yan kasuwa da sauran manyan kasa.

Gwamna Fintiri ya nada sababbin sarakuna

Kun ji cewa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya naɗa wasu sababbin sarakuna a masarautu bakwai da ya kirkiro a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Rusau: Majalisar dokokin jihar Kano ta dauki zafi bayan kisan mutum 4

Gwamna Ahmadu Fintiri ya taya sababbin sarakunan murna tare da rakon su zama masu gaskiya da rikon amana a mulkinsu.

Wannan dai na zuwa ne bayan kirkiro masarautu bakwai a Adamawa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan karfin ikon Lamido.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.