Shugaba Tinubu Ya Waiwayi Bangaren Lafiya, Ya Yi Wa Likitoci da Sauran Ma'aikata Gata

Shugaba Tinubu Ya Waiwayi Bangaren Lafiya, Ya Yi Wa Likitoci da Sauran Ma'aikata Gata

  • Likitoci da sauran ma'aikatan lafiya a Najeriya za su warwasa sakamakon sabon tsarin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi
  • Shugaba Tinubu ya amince da ƙara yawan shekarun yin ritaya ga likitoci da sauran ma'aikatan lafiya a ƙasar nan daga shekara 60 zuwa 65
  • Ministan lafiya, Farfesan Ali Muhammad Pate ya sanar da amincewar yayin wani taro da shugaban ƙungiyar NMA da sauran masu ruwa da tsaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki matakin inganta yanayin aiki na likitoci da sauran ma'aikatan lafiya a Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙara shekarun yin ritaya ga likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya daga shekara 60 zuwa 65.

Tinubu ya inganta yanayin aikin likitoci
Shugaba Tinubu ya kara yawan shekarun ritaya ga likitoci Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA), Dr. Mannir Bature, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Legas, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Hukumar NAHCON ta kara wa'adin biyan kudin hajjin 2025, ta ba maniyyata shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ƙara shekarun aikin malaman asibiti

Mannir Bature ya ce an umarci ministan kiwon lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ya gabatar da amincewar ta hannun ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya domin kammala tsarin.

Ya bayyana cewa Muhammad Pate ya sanar da wannan sabon tsarin ne a lokacin wani taro da shugaban ƙungiyar NMA, Farfesa Bala Audu da sauran manyan masu ruwa da tsaki a ɓangaren kiwon lafiya.

Mannir Bature ya ƙara da cewa, taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyoyin MDCAN, JOHESU da NANNM.

A cewarsa, tattaunawar ta mayar da hankali ne kan ci gaban da aka samu wajen kyautata jin daɗin likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya a Najeriya.

Shugaba Tinubu zai biya likitoci haƙƙoƙinsu

Mannir Bature ya bayyana cewa ministan ya tabbatar da cewa an shirya biyan ragowar kuɗin da ma'aikata suka biyo, sakamakon fito da sabon tsarin albashin likitoci na CONMESS.

“An samar da dukkanin kuɗin da ake da buƙata, kuma nan ba da jimawa ba za a fara turawa waɗanda suka cancanta."

Kara karanta wannan

"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala

- Mannir Bature

Mannir Bature ya ambato ministan yana cewa Shugaba Tinubu ya amince da gyara tsarin albashi na CONMESS da CONHESS, sakamakon fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamnatin Tinubu ta amince da aikin N80bn a Borno

A wani labarin kuma, kun jo cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu, ta amince da aikin gyara madatsar ruwa ta Alau a jihar Borno.

Aikin gyara madatsar ruwan wacce ta ɓalle a shekarar 2024, zai laƙume N80bn za ɗauki tsawon watanni 24 ana yinsa, kafin a kammala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng