Tinubu Ya Gana da Aminu Ado Bayero, Ya ba Shi Tabbacin Kawo Karshen Matsaloli a Kano

Tinubu Ya Gana da Aminu Ado Bayero, Ya ba Shi Tabbacin Kawo Karshen Matsaloli a Kano

  • Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya gana da Bola Ahmed Tinubu a sirrance, mintuna kadan kafin shugaban ya tashi zuwa Faransa
  • Rahotanni daga ɓangaren basaraken sun tabbatar da cewa tattaunawar ta shafi rikicin da ya faru a Rimin Zakara a Ungogo da ke jihar Kano
  • Yayin ganawar, Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna damuwarsa kan kashe mutane hudu da raunata wasu a lokacin da ake neman ruguza gidaje
  • Daga bisani, Bola Tinubu ya ba Aminu Ado tabbacin warware matsalar filin da ake takaddama a kai tsakanin jami'ar Bayero da jama'a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gana da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu.

Rahotanni suka ce basaraken ya gana da Tinubu sirrance, mintuna kadan kafin shugaba ya tashi zuwa Faransa.

Kara karanta wannan

Duk da korafe korafe kan masarautu, Gwamna ya nada dan uwan Nuhu Ribadu sarauta

Abin da Tinubu ya fada wa Aminu Ado Bayero a Abuja
Aminu Ado Bayero ya samu damar ganawa da Bola Tinubu a Abuja kan matsaloli a Kano. Hoto: Masarautar Kano, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Sakataren yada labarai na sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya fitar da sanarwa a yau Laraba, cewar Leadership Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan rushe wasu gidaje da aka yi a Rimin Zakara da al'umma da dama ke ganin an zalunci mutane da ya jawo rasa rayuka.

Abba Hikima ya kalubalanci gwamnatin Kano

Fitaccen lauya, Abba Hikima, ya bayyana damuwarsa kan yadda jami’an tsaro suka gudanar da rusau a yankin, wanda ya kashe mutane.

Ya zargi jami’ar Bayero da sakaci, yana mai cewa sun bar jama’a su gina gidaje sama da 10, 000 a wurin ba tare da an sanar da su rikicin filin ba.

Baristan ya bukaci gwamnatin Abba Kabir Yusuf da ta gudanar da bincike mai zurfi kan yadda aka rasa rayuka a rushe-rushen don daukar mataki.

An yi hasashen dalilin ganawar Tinubu, Aminu Ado

Sanarwar ta ce ana sa ran ganawar ba ta rasa nasaba da rikicin Rimin Zakara, Ungogo da ke jihar Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba sakataren APC a Kano Babban muƙami bayan minista ya bar kujerar

A cewar sanarwar, Aminu Ado ya nuna damuwa kan halin da jama’a ke ciki, musamman kisan mutane hudu da rushe gidaje 50 a rikicin yankin.

Sai dai Tinubu ya tabbatar wa da basaraken cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin warware matsalar rikicin filin da ake takaddama a kai.

Aminu Ado Bayero ya ziyarci Sarkin Bauchi

A baya, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara jihar Bauchi domin halartar babban taro, tare da nuna godiya ga Sarkin da majalisarsa.

Aminu Ado ya jaddada cewa jarabawa daga Allah SWT ne kuma ya yi kira ga mutane su ci gaba da addu'a don samun mafita mai alheri.

Basaraken ya yi addu'ar Allah ya kawar da duk wata matsala, ya kuma gode wa jama'a bisa addu'o'in su da goyon baya ga masarautar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel