An Kama Matsafa da Kokon Kan Dan Adam, Farar Kaza da Farin Kyalle

An Kama Matsafa da Kokon Kan Dan Adam, Farar Kaza da Farin Kyalle

  • Rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo ta kama mutane uku da kokon dan Adam a yankin Ogii, karamar hukumar Okigwe da ke jihar Imo
  • Wadanda ake zargin sun bayyana cewa wani malamin tsibbu ne ya umarce su da su nemo kawunan dan Adam don maganin rikicin filaye
  • Rahotanni sun tabbatar darundunar ‘yan sanda ta fara bincike tare da gudanar da gwaji domin gano asalin mamacin da aka cire kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Imo - Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta kama wasu mutum uku da ake zargin suna da alaka da kokon kan dan Adam da aka samo a yankin Ogii, karamar hukumar Okigwe.

Wadanda ake zargin sun hada da Patrick Okoere, Ifeanyichukwu Anyaemeka da Chukwuemeka Onyekachi dukkansu daga Amasiri a karamar hukumar Afikpo ta jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Barazanar tsaro: An kama 'yan kasashen waje 165 da shirin kulla makirci a Najeriya

Jihar Imo
An kama matasa dauke da kan dan Adam. Hoto: @chekwube_henry
Asali: Twitter

Kakakin ‘yan sandan jihar Imo, DSP Henry Okoye, ya wallafa a X cewa an kama wadanda ake zargin ne a ranar Litinin, 3 ga Fabrairu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa an kama su ne bayan samun rahoton sirri daga wasu mazauna yankin.

Me za a yi da kokon kan dan Adam?

DSP Okoye ya ce bayan kama wadanda ake zargin, sun bayyana cewa wani mutum mai suna Osunta Oko, wanda shi ne kawun Patrick, ne ya umarce su da su nemo kan dan Adam.

Sun kara da cewa Osunta Oko ya bukaci kayin mutum ne domin amfani da shi wajen warware rikicin filaye da yake fuskanta.

"Mun samu kokon kan dan adam tare da kaji da wasu farare tufafi da ake zargin suna da alaka da tsafi.
"Wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun samo kokon kan ne a bakin kogi da ke gefen titin Okigwe-Umuahia, wuri da ake yawan samun rahotannin garkuwa da mutane."

Kara karanta wannan

Sojoji sun kama motar makamai da ake zargi za a mika ga 'yan bindiga

- DSP Okoy

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa yankin da aka kama su yana daga cikin wuraren da ake fuskantar matsalolin tsaro, musamman garkuwa da mutane.

Bincike da matakan tsaro da aka dauka

DSP Okoye ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda ta fara farautar Osunta Oko, wanda ake zargin ya umarci matasan da su samo kokon kan.

Leadership ta wallafa cewa 'yan sanda za su gudanar da gwajin DNA domin gano asalin mamacin da aka samo kokon kansa a hannun mutanen.

"Rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo na ci gaba da gudanar da bincike domin gano asalin mamacin tare da kama duk wasu da ake zargin suna da hannu a wannan lamari.
"Gwajin DNA zai taimaka mana wajen tabbatar da wanda aka kashe aka cire kansa."

DSP Okoye

Ya kara da ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo, CP Aboki Danjuma, ya tabbatar da kudurin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga kauye cikin dare sun yi wa mutane yankan rago

"Rundunar ‘yan sanda za ta tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya bayan kammala bincike.
"Muna kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahotannin da za su taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro,"

- DSP Okoye

'Yan sanda sun kashe yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar hallaka wasu 'yan bindiga a yankin Alkaleri.

Lamarin ya faru ne bayan 'yan sanda sun gwabza fada a wata maboyar 'yan ta'addar da ta hada iyaka da jihohin Gombe da Taraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng