Mummunar Gobara Ta Tashi a Makarantar Allo, An Samu Asarar Rayukan Dalibai

Mummunar Gobara Ta Tashi a Makarantar Allo, An Samu Asarar Rayukan Dalibai

  • An shiga jimami da alhini a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya bayan tashin wata mummunar gobara da daddare
  • Gobarar da ta tashi a wata makarantar allo da ke garin Kauran Namoda, ta jawo asarar rayukan ɗalibai waɗanda adadinsu ya kai mutum 17
  • Bayan asarar rayukan ɗaliban da aka samu, wasu mutanen kuma sun samu raunuka daban-daban, an garzaya da su zuwa asibiti domin kulawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - An samu tashin gobara a wata makarantar allo da ke Kauran Namoda a jihar Zamfara.

Aƙalla dalibai 17 na makarantar allon sun rasa rayukansu sakamakon gobarar wacce ta tashi da daddare.

Gobara ta tashi a Zamfara
Mummunar Gobara ta tashi a makarantar allo a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gobara ta tashi a makarantar allo

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gari gari, sun kashe bayin Allah duk da gwamna ya yi sulhu da su

Majiyoyi sun bayyana cewa mummunan al’amarin ya faru ne a daren ranar Talata, 4 ga watan Fabrairun 2025.

Sun bayyana cewa mummunar gobarar ta ci gaba da ruruwa har na tsawon kusan sa’o’i uku kafin daga baya a samu damar shawo kanta.

Baya ga mutanen da suka rasu, wasu ɗaliban da dama sun samu raunuka kuma a halin yanzu ana ba su kulawa a asibiti.

Shaidun gani da ido sun bayyana gobarar a matsayin wata babbar masifa, inda suka ce ƙoƙarin kashe ta ya gamu da cikas saboda ƙarfin wutar wacce ke ci sosai.

Hukumomin yankin da jami’an bayar da agajin gaggawa sun isa wurin don taimakawa, amma kafin isowarsu, gobarar ta riga ta haddasa babbar asara.

Mutane sun shiga jimami da alhini

Wannan mummunan lamari ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da alhini, musamman dangane da rayukan mutanen da suka salwanta.

Akwai buƙatar hukumomi su binciki musabbabin tashin gobarar domin kaucewa faruwar irin hakan a nan gaba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki

Gobara ta tashi a gidan mai a Adamawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tankokin dakon man fetur sun fashe a wani gidan mai da ke jihar Adamawa a yankin Arewa.

Lamarin wanda ya auku a gidan mai na MRS da ke kan titin Numan a cikin birnin Ƴola, ya jawo an samu tashin gobara.

Tankokin guda biyu da lamarin ya ritsa da su sun ƙone ƙurmus bayan tashin gobarar,wacce ta sanya aka rufe titin shiga birnin Yola.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng