Hukumar NAHCON Ta Kara Wa'adin Biyan Kudin Hajjin 2025, Ta ba Maniyyata Shawara
- Hukumar Alhazai ta amsa kiraye-kirayen da aka yi na ƙara wa'adin lokacin biyan kuɗin aikin Hajjin shekarar bana watau 2025
- Shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar da cewa an ƙara wa'adin zuwa ranar, 10 ga watan Fabrairun
- Ƙara wa'adin lokacin biyan kuɗin ya biyo bayan taron da shugaban hukumar NAHCON ya yi da masu ruwa da tsaki a ranar Talata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), ta sanar da ƙara wa'adin lokacin biyan kuɗin Hajji na shekarar 2025.
Shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya sanar da ƙara wa’adin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, 2025.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanya a shafin X na NAHCON.

Kara karanta wannan
"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NAHCON ta ƙara lokacin biyan kuɗin Hajji
Ta ce matakin ƙara wa'adin ya biyo bayan roƙon da aka yi a madadin wasu maniyyata da ba su kammala rajistarsu ba, kafin wa’adin da aka sanya tun da farko na ranar, 31 ga watan Janairu, 2025.
An cimma matsayar ƙara wa'adin biyan kuɗin ne yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a ranar Talata da daddare.
Shugaban na NAHCON ya yi kira shugabannin hukumomin jin daɗin Alhazai na jihohi da su haɗa kai da hukumar domin tabbatar da cewa an biya kuɗaɗen a kan lokaci.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya bayyana cewa biyan kuɗin a kan lokaci, na da muhimmanci wajen samun masaukai a Saudiyya.
"Shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya sanar da ƙara wa’adin yin rajistar aikin Hajjin 2025 zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, 2025.”
"Yana da matuƙar muhimmanci a sani cewa Saudiyya ta sanya ranar 14 ga Fabrairu, 2025, a matsayin wa’adin ranar kammala sanya hannu kan yarjejeniyoyi."
"Hakan na nufin cewa dole ne duk wasu kuɗin da aka biya su isa asusun IBAN da aka keɓe a Saudiyya kafin wannan rana domin a gane su a dandalin rajistar e-track (Nusuk Masar)."
"La’akari da lokacin da ake buƙata wajen aikawa da kuɗaɗe ƙetare, yana da matuƙar muhimmanci a biya kuɗin da wuri."
- Fatima Sanda Usara
Hukumar NAHCON ta ba maniyyata shawara
A gefe guda kuma, kwamishinan ayyuka na NAHCON, Prince Anofiu Elegushi, ya ba da shawarar cewa maniyyatan da ke da ikon biyan kuɗin Hajji su biya kuɗaɗensu kafin samo kuɗaɗen guzuri.
Har ila yau, Anofiu Elegushi ya nuna cewa wasu maniyyatan sun samu naƙasun N200,000 ne kawai, wanda hakan ya hana su kammala biyan kuɗinsu kafin a kulle rajistar.
EFCC ta kai samame a hedkwatar NAHCON
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC sun kai samame a hedkwatar hukumar NAHCON da ke birnin tarayya Abuja.
Jami'an na EFCC sun kai samamen ne a binciken da suke yi kan zargin karkatar da N90bn na tallafin aikin Hajjin 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng