'Ba Su Kai 900 ba': Kaduna Electric Ya Fadi Adadin Ma'aikatan da Ya Kora daga Aiki
- Kamfanin rarraba wutar lantarki na kewayen Kaduna, watau Kaduna Electric, ya musanta rahoton cewa ya sallami ma'aikata 900 daga aiki
- Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto kungiyar NUEE ta tsunduma yajin aiki saboda korar ma'aikatan KAEDCO da hana su fansho
- Amma a bayanin da KAEDCO ya yi, ya tabbatar da cewa ma'aikatan da ya kora ba su kai 900 ba kuma ya yi hakan saboda matsalar kudi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Mazauna Kaduna da jihohin makwabta na ƙarƙashin Kaduna Electric sun kwashe kwana biyu a duhu saboda yajin aikin ma’aikata.
Legit Hausa ta rahoto cewa kungiyar NUEE ce ta jagoranci shiga yajin aikin da aka fara daga ranar Litinin don nuna rashin amincewa da korar ma’aikata 900.

Source: Twitter
An zargi KAEDCO da tauye hakkin ma'aikata

Kara karanta wannan
Dan Bello ya magance matsalar ruwa a kauyukan Katsina, ya jefa kalubale ga Buhari
Sauran dalilan sun haɗa da rashin biyan fansho, rashin ƙarin girma, ƙarancin kayan aiki, da rashin aiwatar da mafi ƙarancin albashi, inji rahoton Daily Trust.
Da yake magana da manema labarai, shugaban NUEE na Kaduna, Kwamared Sheyin Nuhu Wakili, ya ce dole a biya hakkokin ma’aikatan kafin sallamarsu.
Ya kuma bayyana cewa kamfanin KAEDCO ya amince zai janye sallamar da ya yi wa ma'aikatan, amma abin mamaki sai suka ji an bayar da takardun sallamar.
KAEDCO ya magantu kan sallamar ma'aikata
Yayin da NUEE ta dage cewa mutum 900 aka sallama, hukumar KAEDCO ta fito ta karyata hakan, inda ta ce ma’aikata 450 kawai aka bai wa takardar kora.
A martaninsa, shugaban sashen hulɗa da jama’a na KAEDCO , Abdulazeez Abdullahi, ya ce sun yi hakan a shirin gyara tsarin kamfanin don dorewar aikinsa.
Kamfanin ya kuma tabbatar wa jama’a cewa zai kasance mai fito da komai a fili, tare da tabbatar da adalci ga dukkanin ma’aikata da kwastomominsa.
KAEDCO zai samar da karin 40MW na wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kamfanin KAEDCO ya ce zai samar da karin 40MW na wutar lantarki cikin watanni 18 a jihohin Kano, Jigawa da Katsina.
Hakazalika, kamfanin zai kaddamar da sababbin hanyoyin biyan kudin wuta don magance karkatar da kudaden shiga daga hannun abokan huldar kamfanin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
