Dakarun Sojoji Sun Yi Dirar Mikiya kan 'Yan Ta'adda, Sun Hallaka Miyagu Masu Yawa
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP a jihar Borno da ke yankin Arewacin Najeriya
- Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda guda bakwai tare da ƙwato makamai masu tarin yawa a farmakin da suka kai maɓoyarsu
- Nasarar da sojojin suka samu ta nuna irin jajircewa da ƙoƙarin da suke yi na kawo ƙarshen ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai tare da haɗin gwiwar jami'an CJTF, sun ragargaji ƴan ta'adda a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun kashe ƴan ta’adda bakwai tare da ƙwato makamai a wani samame da suka kai kan maɓoyar ƴan ta'addan ISWAP/Boko Haram a garin Gura Ba, cikin ƙaramar hukumar Bama, a jihar Borno.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakarun sojoji sun farmaki ƴan ta'adda
Wata majiyar leƙen asiri ta bayyana cewa jami'an tsaron sun kai samamen ne a ranar 4 ga watan Fabrairu, 2025.
"A lokacin farmakin, dakarun sojojin sun ci karo da ƴan ta’adda, lamarin da ya kai ga hallaka guda bakwai daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere."
- Wata majiya
Majiyar ta bayyana cewa dakarun sojojin sun ƙwato manyan makamai da dama, waɗanda suka haɗa da, bindigogi guda biyu ƙirar AK-47, bindigogin RPG guda huɗu da alburusai 920 masu kaurin 12.7 x 108mm.
Sauran sun haɗa da alburusai guda shida masu kaurin 7.62mm, harsasai guda 14 masu kaurin 5.6mm da bindiga ƙirar gida guda ɗaya.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa ba a samu rauni ko asarar rai daga ɓangaren dakarun sojojin ba, yayin artabun da suka yi da ƴan ta'addan.
Sojoji na ci gaba da ragargazar ƴan ta'adda
Wannan nasara wani babban ci gaba ne a yunƙurin sojojin Najeriya na murƙushe ragowar ƴan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.
Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai na ci gaba da fatattakar ƴan ta’addan tare da tabbatar da samar da tsaro ga al’ummar yankin.
A baya-bayan nan, sojoji sun ƙara matsa lamba kan ƴan ta'addan ISWAP/Boko Haram, inda suke kakkaɓe sansanoninsu da lalata kayan aikinsu domin hana su farmakar jama'a.
Ana fatan ƙoƙarin sojojin zai taimaka wajen kawo ƙarshen hare-haren ƴan ta’adda da dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na Najeriya sun yi ruwan wuta kan ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan na Boko Haram masu yawa bayan sun jefo musu tarin bama-bamai a sansaninsu da ke ƙaramar hukumar Gwoza.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

