'Ba Ni da Hannu a ciki, Tsohon Gwamna Ya Musanta Zargin Kisan Tsohon Minista a Najeriya

'Ba Ni da Hannu a ciki, Tsohon Gwamna Ya Musanta Zargin Kisan Tsohon Minista a Najeriya

  • Tsohon gwamna Rashidi Ladoja, ya karyata zargin Bisi Akande cewa yana da hannu a kisan Bola Ige, yana mai cewa bai hana shari’a gudanar da aikinta ba
  • Ladoja ya bayyana cewa gwamnatinsa ta goyi bayan shari’ar har zuwa kotun koli, kuma bai san komai game da lamarin fiye da bayanan da jama’a suka sani ba
  • Dattijon ya gargadi Akande da ya janye maganarsa tare da bayar da hakuri, idan ba haka ba kuwa zai ɗauki matakan doka don kare kansa daga wannan zargi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ibadan, Oyo - Tsohon Gwamnan Jihar Oyo kuma Otun Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, ya karyata zargin da hannu a kisan Bola Ige.

Ladoja na magana ne bayan tsohon Gwamnan Osun, Bisi Akande, ya zarge shi da hannu kan kisan tsohon ministan shari'a a gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

"Ka hakura da siyasa," Jama'a sun fara tsoma baki a kan rikicin El Rufa'I da Uba Sani

Ladoja ya musanta zargin hannu a kisan Bola Ige
Tsohon gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja ya ƙaryata zargin hannu a kisan tsohon minista, Bola Ige. Hoto: Rashidi Ladoja.
Source: Facebook

Tsohon gwamnan Oyo ya musanta zargin kisa

Ladoja ya ce bai hana shari’a gudanar da aikinta ba, kuma gwamnatinsa ta bayar da cikakken goyon baya ga shari’ar har zuwa kotun koli, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ya nuna damuwa cewa wasu mutanen da za su iya bayar da bayani, kamar tsohon Gwamnan Oyo, Lam Adesina, sun riga mu gidan gaskiya.

A martaninsa, Ladoja ya yi watsi da zargin, yana mai cewa bai san komai fiye da bayanan da aka fitar ga jama’a ba.

Ladoja zai ɗauki matakin shari'a kan Akande

"An kashe Bola Ige ranar 23 ga Disamba, 2001, ni kuwa na zama gwamna ne ranar 29 ga Mayu, 2003, bayan wata 18."
"Ba ni da hannu a janye shari’ar, gwamnatina ma ta ci gaba da bin shari’a har zuwa kotun koli, Bisi Akande ya yi mani ƙarya."
"Ba mu farin ciki da mutuwar Bola Ige, kuma mun damu da lamarin, Na kasance kusa da shi kafin rasuwarsa."

Kara karanta wannan

'Munafurcin siyasa ba na irinmu ba ne': El Rufai ya sake ta da kura, ya jaddada matsayarsa

- Rashidi Ladoja

Ladoja ya ce zai ɗauki matakan da suka dace, ciki har da na doka, matuƙar Akande bai janye maganarsa ba tare da bayar da hakuri, Punch ta ruwaito.

Matar tsohon gwamnan Oyo ta rasu

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya yi babban rashi bayan rasuwar daya daga cikin matansa.

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar marigayiyar mai suna Tinuade Ladoja a ranar Litinin 14 ga watan Oktoban 2024.

Marigayiyar ta rasa ranta ne tana da shekaru 71 a duniya bayan ta sha fama da jinya a birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.