Gwamnatin Jigawa Ta Ware wa 'Yan Majalisa N30bn don Yaki da Talauci
- Gwamnatin jihar Jigawa ta ware sama da N30 biliyan domin ayyukan ci gaban mazabu na ‘yan majalisar dokoki domin taimakon talakawa
- Akalla mutane 38,250 ne ake sa ran za su amfana da shirin tallafin kudi, inda aka raba kudin ga mutane sama da 2,000 a zagayen farko
- Gwamna Umar Namadi ya bada tabbacin cewa za a ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a sauran mazabu 29 da ke fadin jihar Jigawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin jihar Jigawa ta ware sama da Naira biliyan 30 domin ayyukan mazabu na ‘yan majalisar dokoki.
A karkashin wannan sabon shiri, kowane daga cikin mambobin majalisar guda 30 zai samu wani adadin kudi da za a rarraba a mazabunsu.

Asali: Twitter
Hadimin Gwamna Umar Namadi kan kafafen yada labarai na zamani, Garba Mohammed, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa akalla mutane 38,250 ne ake sa ran za su ci gajiyar shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen karfafa wa marasa karfi da 'yan kasuwa, domin bunkasa tattalin arzikin yankunan.
Gwamnati za ta taimaka wa mazabun Jigawa
Gwamna Umar Namadi ne ya kaddamar da zagayen farko na shirin a garin Mig, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Haruna Aliyu Dangyatin.
Garba Mohammed ya tabbatar wa Legit cewa Gwamna Namadi ya bada tabbacin cewa za a aiwatar da irin wannan shirin a sauran mazabu guda 29 da ke fadin jihar.
Gwamnatin Jigawa na shirin taimakon jama'a
Gwamna Umar Namadi ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da tallafawa al’umma, yana mai cewa duka bangarorin zartaswa da na majalisa suna aiki tare don rage radadin talauci.
A cewarsa:
"Wannan shiri alama ce ta yadda majalisar dokoki karkashin jagorancin Kakakinta ke da kusanci da al’umma, wanda ya sa su ke fahimtar matsalolin da suke fuskanta.
Gwamnatin jihar Jigawa za ta ciyar da azumi
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Jigawa ta sanar da shirin ciyar da mutane 189,000 a fadin jihar a watan azumin Ramadan na shekarar 2024, a kan kudi sama da Naira biliyan 4.8.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Sagir Musa, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a daren Litinin, bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng