KAEDCO: Ana Fama da Matsin Rayuwa, An Kori Ma'aikata Kusan 1,000 a Kaduna

KAEDCO: Ana Fama da Matsin Rayuwa, An Kori Ma'aikata Kusan 1,000 a Kaduna

  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na kewayen Kaduna watau KAEDCO ya sallami ma'aikata 900 daga aiki, lamarin da ya fusata NUEE
  • Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki (NUEE) ta shiga yajin aiki kuma ta fito zanga-zangar nuna adawa da wannan mataki na kora a KAEDCO
  • Sai dai mai magana da yawun kamfanin ya ce waɗanda aka kora ba su kai 900 kamar yadda masu zanga-zangar suka yi ikirari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Al'ummar jihar Kaduna sun shiga duhu bayan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na jihar (KAEDCO) ya kori ma’aikata 900.

Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin ya fara raba takardun sallamar aiki tun ranar Asabar har zuwa Lahadin da ta gabata.

Taswirar Kaduna.
Ma'aikatan wutar lantarki sun shiga yajin aiki kan korar abokansu 900 a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

The Nation ta ce a ranar Litinin, ƴan ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE) suka fara yajin aikin sai baba ta gani don nuna adawa da korar.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara sayar da buhun shinkafa a kan N40000, an kafa sharadi ga ma'aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga ta barke kan korar ma'aikata

Sun kuma fita zanga-zanga a hedikwatar kamfanin da ke kan titin Ahmadu Bello, Kaduna, suna rera wakokin adawa da matakin korar ma'aikata.

Fustattun ma’aikatan sun ɗaga alluna masu rubuce-rubuce daban-daban, sun kuma toshe kofar shiga hedikwatar kamfanin, suka hana ma’aikata da abokan hulɗa shiga.

Ƙungiyar NUEE reshen Kaduna ta zargi shugabannin kamfanin KAEDCO da rashin adalci da kuma take duk wata yarjejeniya da aka cimma.

Kamfanin KAEDCO ya karya alƙawari

Shugaban NUEE na jihar Kaduna, Kwamared Sheyin Nuhu Wakili, ya shaida wa manema labarai cewa:

“Yayin da muke kokarin warware matsalolin da ake fuskanta, shugabannin KAEDCO sun kori manyan ma’aikata 10 ba tare da bin ka’idojin aikin kamfanin ba.
"Duk da shiga tsakani da yarjejeniyoyin da aka cimma a tarurruka da suka gabata, haka kamfanin ya yi fatali da komai, ya ƙi aiwatar da su yadda ya kamata.
"Abin mamaki, mun samu labarin cewa shugabannin sun fara sallamar ma'aikata sama da ma’aikata 900."

Kara karanta wannan

Jama'a sun farmaki masu lalata wutar Najeriya cikin dare, an kama wani ja'iri

Rahotanni sun nuna cewa kusan kowane yanki a jihar Kaduna ya fada cikin duhu sakamakon wannan yajin aiki na ma'aikatan wutar lantarki.

Kamfanin KAEDCO ya musanta korar mutum 900

Sai dai shugabancin kamfanin ya musanta cewa adadin ma’aikatan da abin ya shafa ya kai 900 kamar yadda NUEE ta bayyana.

Shugaban sashen hulda da jama’a na KAEDCO, Abdulazeez Abdullahi, ya shaida wa jaridar Punch cewa za a warware matsalar gaɓa ɗaya ranar Talata.

A cewarsa:

“Za a warware komai gobe. Amma adadin ma’aikatan da korar ta shafa bai kai 900 ba kamar yadda suke ikirari."

Wani tela da ke amfani d keken dinki ta wuta a Kaduna ya tabbatarwa Legit Hausa cewa suna fama da rashin wuyar lantarki a ƴan kwanakin nan.

Ibrahim Yakubu, wanda ake kira da IB ya ce sun samu labarin matsalar da ke faruwa a kamfanin raba wuta kan korar ma'aikata, ya bukaci a sasanta da wuri.

Kara karanta wannan

"Daga Amurka aka samo kudin," Dattijo ya tona yadda aka nemi hana Tinubu takara

Telan ya ce:

"Dama dai kwana biyu wuta ba ta zama, ga tsadar fetur idan aka tafi a haka akwai matsala.
"Jiya muna zaune wani yake bamu labarin ma'aikatan wutar sun shiga yajin aiki, a gaskiya wannan ba ƙaramar matsala ba ce a kasuwancin mu, ya kamata a ɗauki mataki.

TCN ya jero barazanar da yake fuskanta

A wani labarin, kun ji cewa Kamfanin Wutar Lantarki watu TCN ya bayyana cewa an lalata turakun wutar lantarki akalla guda 18 wanda ya jawo rashin wuta a ƙasa.

TCC ya ce wannan lamari na lalata kayan wuta na daga cikin babbar barazanar da kamfanin ke fuskanta a ƙoƙarin wadata ƴan Najeriya da wutar da lantarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262