'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Sarki da Wasu Mutane 5, Sun Kashe Mutum 1 daga ciki
- Ana zargin wasu miyagun yan bindiga sun tare basarake a kan titi, sun yi awon gaba da shi bayan halaka ɗan acaɓar da ya ɗauko shi a jihar Edo
- Bayan sace Mai Martaba Friday Ehizojie, an kuma yi garkuwa da wasu mutum biyar, amma daya daga cikinsu ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane
- Kwamishinar ‘yan sanda ta bada umarnin tura jami’an tsaro domin tabbatar da kubutar da wadanda aka sace da kuma kamo wadanda suka aikata laifin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Wasu ‘yan bindiga sun sace Mai Martaba Friday Ehizojie, Onojie, sarkin gargajiya na masarautar Udo-Eguare da ke karamar hukumar Igueben, a jihar Edo.
Rahotanni sun nuna cewa an sace basaraken a daidai wani daji da ke tsakanin ƙauyen Ubiaja, kusa da Rest House Junction da kauyen Udo.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan bindigar sun buɗe wuta bayan sun tare basaraken, suka bindige wani ɗan acaba har lahira kafin su tafi da sarkin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan bindigar sun haɗa da mutum 5
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa maharan sun kuma haɗa da wasu mutum biyar, sun yi awon gaba da su zuwa maɓoyarsu da ba a sani ba.
Sai dai a cewar majiyar, ɗaya daga cikin mutane biyar da maharan suka sace tare da sarkin ya kuɓuto, ya dawo gida.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Moses Yamu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.
Yan sanda sun tabbatar da sace basarake
Ya ce rundunar ƴan sanda ta samu rahoton sace wasu mutane, ciki har da mai martaba Onogien na Udo-Eguare da wani matashi dan shekara 21.
Mai magana da yawun rundunar ya ce:
"Mai martaba yana kan babur ne a matsayin fasinja a wata hanya da ba a cika bi ba zuwa garin, sai kawai ‘yan bindiga suka yi masa kwanton bauna, suka harbe direban babur, sannan suka yi garkuwa da shi.”

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun nuna kwarewa, sun ceto mutanen da 'yan bindiga suka sace a Kaduna
Kwamishina ta tura dakaru na musamman
Moses Yamu ya ce kwamishinar ‘yan sanda ta jihar Edo, Betty Otimenyin, ta bada umarnin tura tawagar dakaru na musamman zuwa yankin da lamarin ya auku.
A cewar kakakin ƴan sandan, dakarun da aka tura za su bazama cikin dazukan yankin domin ceto basaraken da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su tare.
Yamu ya ƙara da cewa tuni kwamandan jami'an ‘yan sanda na yankin ya isa wurin kuma shi ke jagorantar atisayen ceto saekin kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda ta umurta.
"Ana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da basaraken da sauran mutanen da aka sace," in ji Moses Yamu.
Yan bindiga sun sace shugaban hukumar zaɓe
Kun ji cewa mahara sun kutsa cikin gida, sun yi awon gaba da shugaban hukumar zaɓe ta jihar Abia, Farfesa George Chima.
An ruwaito cewa ‘yan bindigar, kimanin su huɗu, sun farmaki gidan shugaban hukumar zaɓen ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu malamai daga jami’ar Abia.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng