Bayan Shafe Tsawon Lokaci a kan Sarauta, Kotu Ta Tsige Mai Martaba Sarki a Najeriya
- Babbar kotun jihar Kogi mai zama a Lokoja ta sauke mai martaba sarkin Ebira, Ahmed Muhammed Tijani Anaje daga kan sarauta
- Alkalin kotun, mai shari'a Salisu Umar ya ce ya gamsu da hujjojin da aka gabatar a shari'ar, ya ce matakan da aka bi wajen naɗa sarkin sun saɓa doka
- Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ne ya naɗa Ahmed Anaje a matsayin sarkin Ebira bayan rasuwar Mai martaba Dr. Ado Ibrahim
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi - Babbar kotun jihar Kogi da ke zamanta a Lokoja ta tsige Mai Martaba Ahmed Muhammed Tajani Anaje daga matsayin sarkin Ebira watau Ohinoyi na Ebiraland.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Salisu Umar ne ya yanke wannan hukunci a ranar Litinin, 3 ga watan Fabrairu, 2025.

Asali: Facebook
Ya kuma umarci Ahmed Anaje da ya daina bayyana kansa a matsayin sarkin gargajiya mafi girma a Ebiraland, kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin kai ƙara kotu kan naɗin basaraken
Dr. Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutum biyu ne suka shigar da ƙarar mai lamba HCO/05C/2024 a gaban kotu suna kalubalantar Gwamnan Jihar Kogi da kuma Ahmed Anaje.
Masu karar sun bayyana cewa an samu kura-kurai da rashin bin doka a tsarin da aka bi wajen nada Ahmed Anaje a matsayin Ohinoyi na Ebiraland.
Sun yi zargin cewa an kauce daga tsarin da ya dace kuma an saba ka’idojin nadin sarautar gargajiya na Ebira, rahoton Leadership.
Tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, ne ya nada Ahmed Anaje a matsayin sarkin Ebiraland bayan rasuwar tsohon Ohinoyi, Mai Martaba Dr. Ado Ibrahim.
Kotu ta tsige sarkin Ebira a jihar Kogi
Bayan nazari kan shari'ar da kuma hujjojin masu ƙara, kotu ta yanke hukunci cewa an nada sarkin ba tare da cikakken bin ka’idoji ba, don haka nadinsa bai halatta ba.
Hukuncin kotun ya soke nadin Mai martaba Ahmed Muhammed Anaje, tare da bada umarni cewa a bi tsarin masauratar da tanadin doka wajen zaben sabon Ohinoyi na Ebiraland.
Wannan hukunci na iya haifar da sabon rikici a yankin, amma ana sa ran gwamnatin Kogi da masu ruwa da tsaki za su dauki matakin da ya dace kan lamarin.
Sarkin Lokoja ya ba gwamnati shawari
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Lokoja da ke jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi IV, ya bukaci gwamnati ta bai wa sarakuna mukamai.
Basaraken ya bayyana cewa sarakuna suke kusa da al'umma kuma su suka san matsalolin da talakawa ke fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng