An Kalubalanci Izala kan Gaskiyar Wanda Ya Shirya 'Quran Convention'

An Kalubalanci Izala kan Gaskiyar Wanda Ya Shirya 'Quran Convention'

  • Barista Bulama Bukarti ya nemi malaman Izala da za su jagoranci taron mahaddata a Abuja su bayyana wanda su ka dauki nauyin taron
  • Bukarti ya bayyana cewa an ce Mele Kyari ne ya fara maganar taron, amma kuma ya musanta wata masaniya a kan batun baki daya
  • Bulama Bukarti ya ce 'Qur'an Convention' kamar bidi'a ne idan aka yi amfani da yadda malaman Izala ke sukar wadannan taro a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Sanannen lauya, Barista Bulama Bukarti ya nemi alaman Izala da za su jagoranci babban taron mahaddata a Abuja da su bayyana wanda su ka dauki nauyin taron.

Barista Bulama ya bayyana cewa akwai sarkakiya a cikin wanda su ka dauki nauyin taron, wanda ya ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida Gida ta fadi dalilin kashe N2.5bn a kan auren gata

Bukarti
An nemi sunan wanda ya dauki nauyin 'Qur'an convention' Hoto: Abdu Bulama Bukarti
Source: Facebook

A bidiyon da ya Abdu Bula Bukarti ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa guda daga cikin malaman sunnah, Dr. Jalo Jalingo ya bayyana cewa shugaban NNPCL, Mele Kyari ne ya fara maganar taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kyari ya musanta daukar nauyin 'Qur'an Convention'

Barista Bulama Bukarti ya bayyana cewa sun ji yadda Shugaban Izala na Kaduna, Dr. Jalo Jalingo ya ce Mele Kyari ne ya tara su, sannan ya bijiro masu da batun babban taron.

Ya bayyana cewa sai dai an ji yadda Kyari, ta bakin Mai magana da yawunsa ya barranta kansa daga batun, inda ya ce shi ne ya nemi malaman da su dauko babban taron mahaddata ba.

Bukarti ya ce:

"Ya ce kwata-kwata ba shi da alaka ta kusa ko ta nesa da maganar. Sannan kowanne daga Malaman nan sun ce gayyato su aka yi, kuma su ka ga abu mai kyau ne, haka Izala suka ce, haka Sheikh Dahiru Bauchi ya ce. Amma wanene ya gayyato su?

Kara karanta wannan

"Su na cewa maulidi bidi'a ne," Sarkin Kano ya yi raddi a kan 'Qur'an convention'

Me ya kawo Izala cikin 'Qur'an convention'?

Babban lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Bulama Bukarti, ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne idan aka ji Malaman darika na gudanar da irin wannan taro.

Ya kara da cewa amma yadda aka tsinci Malaman Izala sun yi kane-kane a lamarin ya ba da mamaki matuka, ganin yadda su ke sukar duk wani taro da babu shi a sunnah.

Ya ce:

"To amma idan izala ta zo ta ce za ta yi taron nan, sai ka ce to, ina matsayarku a kan tarurruka da ake yi a baya ku na cewa bidi'a ne. Tun da ko ka na so, ko ba ka so, da farko dai 'Qur'an festival' ya na nufin bikin Kur'ani.

Bulama Bukarti ya kara da cewa ita kanta kalmar 'convention' ta fi kama da taro na siyasa, duk da cewa ana iya amfani da ita a kan duk wani irin babban taro.

Sai dai ya na ganin taron ya fi kama da biki, wanda idan aka bi salsalar abin da malaman Izala su ke tafiya a kai, wannan ya koma bidi'a zalla.

Kara karanta wannan

'Na rasa budurcina': Bobrisky ya fadi yadda ya dirka wa budurwa ciki a jami'a

Sarki Sanusi II ya magantu kan 'Qur'an convention'

A wani labari, mun ruwaito cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana ra'ayinsa game da babban taron mahaddata Al-Kur'ani da kungiyar Izala ta shirya a Abuja.

Sarki Sanusi II ya jaddada cewa ba za a kira taron mahaddata a matsayin bidi'a ba, kamar yadda Izala ke kiran maulidi, sai dai idan aka bi taalaman, za a dauke wannan a matsayin bidi'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng