An Fara Sayar da Wiwi da Siffar Alewar Yara a Kano

An Fara Sayar da Wiwi da Siffar Alewar Yara a Kano

  • Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a Kano ta gargadi iyaye a kan sabuwar alewar wiwi
  • Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sadiq Muhammad ne ya bayyana haka, inda ya ce wannan na zama babbar barazana
  • Ya shawarci jama'a iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da a gaggauta nemo hukumar, da zarar an yi arangama da alewar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargadi iyaye kan yaduwar wasu alawowi da ake zargin suna dauke da kayan maye a cikinsu.

Hukumar ta haska hotunan alewa da ta bayyana cewa wiwi ne aka sauya masu fasali, tare da bayyana hadarin da ke tattare da lamarin da ke barazana ga rayuwar matasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida Gida ta fadi dalilin kashe N2.5bn a kan auren gata

Alewa
NDLEA ta yi gargadin sabuwar alewar wiwi a Kano Hoto: Sadiq Muhammad
Asali: Facebook

Gargadin ya fito ne a wani fefen bidiyo da jami'in hulda da jama'a na hukumar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Maigatari ya bayyana cewa alawar tana kama da cakulan da aka saba sha amma suna dauke da sinadarai da ke sa maye.

Yadda ake sayar da alewar wiwi a Kano

Jami'in hulda da jama'a na hukumar NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya tabbatar wa da Legit cewa ba a ko ina jama'a za su iya sayen alewar ba.

Ya ce masu amfani da ita su na da boyayyiyar hanya da su kan yi cinikinta a tsakaninsu, har ta kai ga hannun matasa da sauran masu amfani da ita.

Ya ce:

"Ba a ko ina a sayar da ita ba, ana amfani da hanyoyi na musamman ne.

NDLEA ta gargadi iyaye a kan alewar wiwi

Hukumar NDLEA ta Kano ta gargadi iyaye da su kara zagewa wajen sanya idanu a kan irin abubuwan da yaransu ke shigowa.

Kara karanta wannan

"Su na cewa maulidi bidi'a ne," Sarkin Kano ya yi raddi a kan 'Qur'an convention'

Sadiw Muhammad Maigatari ya ce:

"Tabar wiwi ce aka sarrafa ta, aka maida ta cikin wannan gida. Abin da iyaye da makusanta za su lura shi ne daga kasan wannan gida na wannan taba, akwai hoton wata fulawa mai yatsu biyar.Wannan fulawa da ku ke gani, to ganyen tabar wiwi ke nan. Sannan daga gefe, za ka inda aka rubuta 'cannabiis flower.'"

Hukumar ta bukaci duk wanda ya ga irin wannan alewa, da su a gaggauta kiranta domin tabbatar da an tsare hankalin matasakan Najeriya.

NDLEA: An gano gonar wiwi a Kano

A baya, mun ruwaito cewa hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya ta gano wata gona da ake noma tabar wiwi, tare da cafke wani dattijo da ake zargi da mallakar gonar.

Mai magana da yawun NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ya wallafa bidiyon hirar da suka yi da Malam Sabo inda aka gan shi a gaban gonarsa da ke cike da bishiyoyin tabar wiwi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.