Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Magana, Ta Ce babu Batun Karin Kudin Wutar Lantarki

Gwamnatin Tarayya Ta Sauya Magana, Ta Ce babu Batun Karin Kudin Wutar Lantarki

  • Fadar Shugaban Kasa ta musanta rahotannin da ke cewa akwai shirin karin kudin wutar lantarki da 65% a kwanan nan
  • Olu Arowolo Verheijen, mai ba shugaba Bola Tinubu shawara kan makamashi, ta bayyana cewa an fahimci kalamanta ba daidai ba
  • Verheijen ta bayyana cewa yanzu haka kudin wutar lantarki da jama'a ke biya 65% ne na kudin da zai samar da wuta ga kasa
  • Yayin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke kokari wajen yin cikon sauran gibin da aka samu, domin kasa ta wadata da wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Fadar Shugaban Kasa ta musanta rahotanni da ke cewa akwai karin 65% na kudin wutar lantarki da ake shirin yi.

Kara karanta wannan

Kowa ya shirya: Gwamnatin Tinubu ta sanya lokacin kara kudin wutar lantarki

Gwamnatin ta bayyana cewa rahotannin da aka yada sun yi kuskure wajen fassara bayanan da aka fitar daga a kan batun karin kudin wuta.

Tinubu
Gwamnati ta musanta shirin kara kudin wuta Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Leadership News ta ruwaito cewa Olu Arowolo Verheijen, mai ba shugaba Bola Tinubu shawara kan batun makamashi, ta yi karin haske kan batun karin farashin wutar a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da mayar da hankali kan inganta bangaren wutar lantarki da kuma kare talakawa daga karin karin da zai gagari aljihunsu.

“An fahimce ni a bai-bai,” Hadimar Tinubu

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dole ne ta yi karin haske kan batun karin farashin kudin wutar lantarki, ganin cewa an dauki bayanan a bai-bai.

Hadimar shugaban Tinubu a kan makamashi ta ce:

“Ya zama dole a fayyace rahotannin da ke nuna cewa za a kara kudin wutar lantarki da 65%. An dauki kalaman da na yi a baya a wata hira a ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu ta ba da mamaki a Kwara, ta fita a mota ta tattauna da dalibai

Ta kara da cewa, yanzu haka kudin wutar lantarki yana rufe kusan kashi 65% na kudin da ake biya wajen samar da wutar, bayan karin kudin 'yan sahun B da A a shekarar 2024.

Ta kara da cewa gibin da ya yi saura kuma, gwamnatin tarayya ce ta ke ci gaba da bayar da tallafin domin a samu damar rarraba hasken wutar ga jama'a.

Hadimar Tinubu: 'Babu shirin kara kudin wuta'

Olu Arowolo Verheijen, mai ba da shawara kan makamashi, ta ce babu wani shiri na karin kudin wutar lantarki ga talakawa.

Ta kara da bayyana manyan abubuwan da gwamnati za ta mayar da hankali a kai wajen inganta bangaren wutar lantarki, ciki har da sanya mita, tallafi na musamman, warware basussuka, da samar da makamashin zamani.

Wutar lantarki: Gwamnatin Tinubu ta karbo bashi

A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da samun bashin Dala biliyan 1.1 daga Bankin Raya Afrika (AfDB) domin inganta samar da hasken wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

Shugaban kasa, Bola Tinubu Shugaba da ya bayyana haka, ya kara da cewa wannan bashi zai taimaka wajen samar da wutar lantarki ga mutane miliyan biyar nan da ƙarshen shekarar 2026.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel