Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Wani Hari a Jihar Taraba

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Wani Hari a Jihar Taraba

  • Ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a wani ƙauyen jihar Taraba da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Miyagun ƴan bindigan waɗanda suka kai harin cikin tsakar dare sun hallaka mutum ɗaya tare da yin garkuwa da wasu mutum tara
  • Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta tabbatar da aukuwar harin wanda ƴan bindigan suka kai a tsakar dare

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun hallaka mutum ɗaya a harin da suka kai a ƙauyen Piroje, cikin ƙaramar Lau ta jihar Taraba.

Haka kuma, ƴan bindigan sun yi garkuwa da mutane tara a harin da suka kai da tsakar dare a ƙauyen.

'Yan bindiga sun kai hari a Taraba
'Yan bindiga sun sace mutane a jihar Taraba Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Asabar, 1 ga watan Fabrairun 2025.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai hari a Taraba

Ƴan bindigan waɗanda sun fi guda 20 sun shiga ƙauyen Piroje ne, wanda ke kusa da ƙauyen Jimlari a kan hanyar Jalingo zuwa Yola, da misalin ƙarfe 2:00 na dare.

Harin ya haifar da firgici, inda mazauna yankin suka tsere zuwa daji domin tsira da rayukansu.

Majiyoyi sun bayyana cewa mata da yara da suka tsere daga harin sun kwana a cikin daji ba tare da matsuguni ba, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan bindigan ba su taɓa dukiya ko sace shanu ba, amma sun tafi da mutane tara, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin al’ummar garin.

Har ya zuwa yanzu, ƴan bindigan ba su tuntuɓi ƴan uwan waɗanda aka sace ba don neman kuɗin fansa.

Ƴan sanda sun yi ƙarin haske kan harin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar harin.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun nuna kwarewa, sun ceto mutanen da 'yan bindiga suka sace a Kaduna

Ya bayyana cewa mutum ɗaya ne aka kashe, yayin da aka sace mutane takwas, saɓanin rahotannin da suka ce mutane tara ne aka yi garkuwa da su.

Jami’an tsaro sun ce suna kan bincike don gano inda ƴan bindigan suka kai mutanen, tare da ɗaukar matakan kuɓutar da su.

Har ila yau, an buƙaci al’ummar yankin da su ci gaba da ba jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da ingantattun bayanai da za su taimaka wajen kamo masu laifin.

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun hallaka mutane biyar a wani harin ta'addanci da suka kai a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Ƴan bindigan sun kai harin ne cikin tsakar dare lokacin da mazauna yankin suke tsaka da barci a cikin gidajensu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng