Mutanen Gari Sun Yi Rugu Rugu da Dan Dabar da Ya Fitini Al'umma a Kano

Mutanen Gari Sun Yi Rugu Rugu da Dan Dabar da Ya Fitini Al'umma a Kano

  • An kama ɗaya daga cikin 'yan daba da ake kira ‘Yan 6’ a Sheka a Kano mai suna Aminu Yusuf bayan haddasa fashi da rikici a unguwar
  • An ruwaito cewa bayan an kama shi, mutane sun yi masa duka har suka karya masa ƙafa ɗaya, sannan suka raunata ɗayar ƙafar sosai
  • Kakakin ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa bayan rasuwar Yusuf Aminu, abokanansa sun fito ɗaukar fansa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rikicin 'yan daba ya sake ɓarke wa a unguwar Sheka da ke cikin birnin Kano, inda aka kashe wani matashi da ake zargi da ta’addanci da fashi da makami.

Matashin da aka kashe mai suna Yusuf Aminu, ɗan ƙungiyar ‘Yan 6’ ne, wanda ya shahara da tada zaune tsaye tare da abokanansa a yankin Sheka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki da wasu mutane 5, sun kashe mutum 1 daga ciki

Dan daba
An kakkarya dan daba a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa|AFP (Getty)
Source: Facebook

A cewar rundunar ‘yan sanda Kano, an kama wadanda ake zargi da hannu a cikin rikicin, kamar yadda SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.

Yadda aka kashe dan daba a Sheka

Rahotanni sun nuna cewa Yusuf Aminu ya shiga hannun jama’a bayan wani rikici da ya ɓarke sakamakon fashi da rikicin daba da suka tayar a bayan makarantar Sheka.

Bayan kama shi, wasu daga cikin mazauna yankin sun yi masa duka har suka karya masa ƙafa ɗaya tare da raunata ɗayar ƙafar sosai. Daga bisani, Yusuf Aminu ya rasu sakamakon raunukan.

'Yan daba sun fito daukar fansa a Kano

Kakakin rundunar ‘yansanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa abokan Yusuf Aminu sun fito domin ɗaukar fansa.

A cewarsa, lamarin da ya jawo sabon rikici tsakanin kungiyoyin daba a Sheka a ranar 2 ga Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta ana rigimar sarauta, an harbi 'yan sanda 7

“Yanzu haka mun kama mutane da dama da ake zargi da hannu a cikin rikicin,”

- SP Abdullahi Haruna Kiyawa

Martanin jama’a kan lamarin

Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka bayyana ra’ayoyinsu kan rikicin da ya yi sanadin mutuwar Yusuf Aminu.

Fairuz Abubakar Khalil ta bayyana cewa:

"Yaron kirki ne wallahi, lokaci ɗaya abokai suka canza shi. Allah ya shirya su, shi kuma Allah ya ji kansa, ya yafe masa kura-kurensa."

Auwal Gano ya kwatanta lamarin da irin abin da ya faru a unguwar Kuwait da ke Tudun Murtala, inda yace:

"Irin haka ya taɓa faruwa, daga bisani ‘yan sanda suka kama ‘yan banga da zargin kisa. Amma mutane ne suka gaji da ‘yan fashi da makami suka kare kansu."

Muhammad Mukhtar Danfillo ya bayyana damuwarsa da cewa:

"Kuna iya kokarin ku wajen magance ‘yan daba, amma sai kun nusantar da shugabannin da suke nunawa al’umma halin rashin da’a. Domin al’umma suna koyo daga shugabanninsu."

Kara karanta wannan

An kama 'yan bindigar da suka ba basarake kudi domin kafa sansanin ta'addanci

Bashir Ibrahim Na’iya ya bayyana cewa:

"Da a ce duk haka ake musu, da an rage marasa amfani a cikin al’umma, kuma da an sami raguwar mugaye a cikin nagari."

Haka zalika, Ummi Adam Rano ta bayyana cewa:

"Wannan fada tsakanin ‘yan Sheka ya jawo fargaba ga mazauna yankin. A kullum cikin tashin hankali muke saboda ayyukan barayi da ‘yan daba."

Auwalu Umar ya ƙara da cewa:

"Allah ya sa wannan ya zama izina ga masu tada zaune tsaye marasa son zaman lafiya, a unguwanni da kuma fadin jihar Kano."

An kama 'yan ta'adda 23 a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya sun kai wani farmaki mabiyar 'yan ta'adda da ake zargin sun ba wani basarake kudi domin kafa sansani.

Bayan kai samamen, an kashe dan ta'adda daya, kama 23 tare da kwato tarin makamai da suka hada bindigogi, babura, adduna, gatari da sauransu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng