Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Hana Zanga Zanga kan Karin Kudin Kira, Ta Kira NLC Taro
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara yunƙurin ganin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ba ta gudanar da zanga-zanga ba
- A bisa ƙoƙarin hana zanga-zangar kan ƙarin kuɗin kira da data da aka amince da shi, gwamnatin ta kira NLC taro domin su tattauna kan lamarin
- Ƙungiyar NLC dai ta shirya gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da ƙarin kuɗin kira da data na kaso 50% da aka amince da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara shirin hana zanga-zangar da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ke shirin yi kan ƙarin kuɗin kira da data.
Gwamnatin tarayyar ta kira shugabannin ƙungiyar NLC domin gudanar da taro a yau Litinin, 3 ga watan Fabrairun 2025.

Asali: Facebook
Gwamnatin tarayya za ta tattauna da NLC
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa za a tattauna kan adawar da NLC ke yi kan ware N8bn a kasafin kuɗin 2025 don wayar da kan jama'a kan biyan kuɗin wutar lantarki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar NLC dai ta bayyana ware kuɗin a matsayin almubazzaranci da cin hanci da rashawa.
Wata majiya daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), wanda ke ɗaukar nauyin taron, ta bayyana cewa an tsara fara taron da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.
Majiyar ta bayyana cewa taron na da nufin tattauna batutuwan da suka shafi buƙatun ma’aikata da kuma ƙarin kudin sadarwa da gwamnatin tarayya ta amince da shi, wanda NLC da sauran ƙungiyoyi suka nuna matuƙar adawa da hakan.
NLC ta fara shirin zanga-zanga
Tuni NLC ta fara jan hankalin ma’aikata don gudanar da zanga-zangar a gobe (4 ga watan Fabrairu) kan ƙarin kuɗin sadarwa da gwamnatin tarayya ta amince da shi.
Haka kuma, taron zai tattauna kan ware N8bn a kasafin kuɗin 2025 domin wayar da kai kan biyan kudin wutar lantarki.
Saboda wasu tarurruka da gwamnati ta riga ta tsara a ranar Litinin, an sanya gudanar da taron bayan taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.
Majiyoyin daga NLC sun bayyana cewa shugabannin ƙungiyar za su halarci taron don jin abin da gwamnati za ta faɗa, amma sun jaddada cewa, babu yadda za a yi su amince da ƙarin kuɗin sadarwa na kaso 50% cikin 100%.
NLC ta faɗi wuraren taruwa lokacin zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga kan ƙarin kuɗin kira da data.
Ƙungiyar NLC ta sanar da wuraren da za a taru a jihohi domin gudanar da zanga-zangar ta gobe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng