Bidiyo: Sarki Ya Ci Mutuncin Wani Tsoho, Ya Tilasta Shi Kwanciya a kan Titi

Bidiyo: Sarki Ya Ci Mutuncin Wani Tsoho, Ya Tilasta Shi Kwanciya a kan Titi

  • Gwamnatin Ogun ta ce za ta binciki wani bidiyo da ya nuna ana cin zarafin wani basaraken jihar, Chief Arinola Abraham Love
  • A cikin bidiyon, an ji wani da ake zargin Sarki Semiu Ogunjobi ne yana yana la’antar Arinola da iyalansa tare da yi masa barazana
  • Jami’an gwamnati sun ce dole ne a bi doka wajen warware rigingimu, ba amfani da karfi ko cin zarafi ba kamar yadda basaraken ya yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta ce za ta binciki wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, inda aka ga ana cin zarafin Cif Arinola Abraham Love.

Ana zargin Oba Semiu Ogunjobi, sarkin Orile Ifo, da yin wannan aika-aika a karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun.

Gwamnatin Ogun ta yi magana da wani sarki ya ci mutuncin basarake a bidiyo
Gwamnatin Ogun za ta binciki zargin cin zarafin wani basarake a cikin bidiyo. Hoto: @DapoAbiodunCON
Asali: Facebook

Sarki ya ci zarafin basarake a cikin bidiyo

Kara karanta wannan

Rikici ya barke da gwamna ya nada sabon sarki, an kashe mutane da dama

A bidiyon mai tsayin mintuna biyu, an ga Cif Arinola yana durƙushe kan gwiwowinsa a kan hanya yayin da wani mutum ke la’antar shi da iyalansa, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Oba Ogunjobi da yin barazanar cewa yana da ikon amfani da ‘yan sanda wajen jefa Cif Arinola a kurkuku ba tare da wata matsala ba.

A bidiyon, sarkin Orile Ifo ya yi barazanar cewa ko da Cif Arinola ya mutu, zai sa a binne shi ba da sanin kowa ba kuma ba abin da zai faru.

Sarkin Orile Ifo ya yi barazanar birne Cif Arinola

Daya daga cikin mutanen da ke tare da shi ya mari Cif Arinola tare da umartar sa da ya kwanta a kasa a gaban basaraken.

Oba Ogunjobi ya yi magana a harshen Yarbanci yana la’antar Cif Arinola da iyalansa bisa zargin cewa shi ma ci amana ne.

Wannan bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a soshiyal midiya wanda har ta kai ga gwamnatin jihar Ogun ta fitar da sanarwa a kai.

Kara karanta wannan

Tubabben dan bindiga da ya tuba ya zama malami, ya jagoranci addu'o'i a bidiyo

Gwamnatin Ogun za ta gudanar da bincike

Mai bai wa Gwamna Dapo Abiodun shawara kan sadarwa, Kayode Akinmade, ya ce wannan abu abin kyama ne kuma ya sabawa doka.

Akinmade ya ce gwamnatin jihar Ogun za ta binciki lamarin, kuma idan har ta gano gaskiya ne, za a dauki matakin da ya dace kan sarkin.

Haka nan, hadimin gwamna kan sababbin kafafen sada zumunta, Emmanuel Ojo, ya ce ana iya warware kowacce matsala cikin lumana.

Ojo ya ce doka ce kadai za ta iya warware rikici tsakanin sarakuna, ba amfani da karfi, cin zarafi ko duka da nuna izza ba.

Kalli bidiyon, wanda jaridar Punch ta wallafa a kasa:

Sarki ya aika sako ga Sarkin Musulmi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Oba Omo Tooyosi Akinleye, wani basarake a yankin Yarbawa ya ika sako ga sarkin Musulmi kan kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Bauchi: Ana zargin kwamishina da sace yarinya, wanda ake tuhuma ya fayyace lamarin

Oba Akinleye ya yi gargadin cewa kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma zai haifar da tashin hankali da rashin jituwa tsakanin Musulman Yarbawa da Kirista ko masu addinin gargajiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel