An farlantawa masu shiga Jami’ar Legas koyon harshen yarbanci
- Daga yanzu sai wanda ya iya Yarbanci zai shiga Makarantu da Jami’a a Legas
- Gwamna Ambode ya sa hannun kan dokar da za ta sa a rika amfani da yarbanci
- Babu wata Jiha cikin Jihohin Najeriya da ta taba kafa wannan doka kawo yanzu
Mun samu labari cewa daga yanzu koyar da yaren Yarbanci a Makarantun boko ya zama dole a Jihar Legas kuma sabawa wannan doka zai jawowa mutum tarar kudi. Kuma sai da yaren za a samu shiga Makarantun Jihar na gaba da sakandare.
An kawo wata doka a Ranar Alhamis da ta wuce da ta wajabta koyar da Yarbanci a Makarantun Bokon Firamare da Sakandaren Gwamnati da ma na ‘Yan kasuwa na Jihar Legas. Gwamna Akinwumi Ambode ya sa hannu a wannan doka.
KU KARANTA: Adam Zango ya sha ruwan duwatsu a Jihar Gombe
Yanzu haka dai Gwamnatin Jihar Legas ta zama ta farko a Kasar da ta wajabtawa jama’a koyon yaren gida. Kwamsishinan shari’a da sauran Kwamishionin Jihar su nan a lokacin da Gwamnan na Legas Ambode ya rattaba hannu kan dokar.
Bayan nan dai Gwamnatin Jihar Legas ta kawo wasu sababbin dokoki har 6 da za su shafi fannin kiwon lafiya da wutan lantarki a Jihar. Sabawa wannan dokar ta aiki da yaren yarbanci a fadin Jihar na iya jawowa mutum tarar N500,000.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng