Dangote Ya Fadi Dalilin Karya Farashin Man Fetur a Najeriya

Dangote Ya Fadi Dalilin Karya Farashin Man Fetur a Najeriya

  • An fara samun bayanai kan dalilin rage farashin man fetur da matatar Dangote ta yi daga N950 zuwa N890 a ranar Asabar da ta gabata
  • Ana alakanta rage farashin da sauƙar kudin danyen mai a kasuwar duniya da kuma kokarin cika alkawarin da Dangote ya yi kan farashi
  • Alhaji Aliko Dangote ya bukaci ‘yan kasuwa su tabbatar da cewa ragin farashin ya amfani jama’ar Najeriya kai tsaye wajen rage musu kudi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Masana sun fara sharhi kan rage farashin man fetur da matatar Dangote ta yi a ranar Asabar.

Bayan sauke farashin, matatar Dangote ta yi kira ga 'yan kasuwa su rage kudin mai domin tabbatar da cewa talakawa sun shaida samun saukin.

Dangote
Dangote ya fadi dalilin rage kudin mai a Najeriya. Hoto: Dangote Industries|NNPC Limited
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa jami'in hulda da jama'a na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina ne ya fitar da sanarwar.

Kara karanta wannan

'Ba yanzu ba': 'Yan kasuwa sun fadi lokacin karya farashin fetur a gidajen mai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa Dangote rage kudin mai?

A ranar Asabar, 1 ga watan Fabrairun 2025 matatar Dangote da ke Legas ta sanar da rage kudin man litar man fetur daga N950 zuwa N890.

Bayan sauke farashin, matatar Dangote ta yi kira ga 'yan kasuwa masu gidajen mai da su rage farashi ga 'yan kasa.

Ragin farashin ya samo asali ne sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya da kuma yanayin ci gaban tattalin arzikin makamashi na duniya.

Dangote ya bayyana cewa wannan sauyin farashi ya kasance ne domin cika alkawarin da kamfanin ya yi na daidaita farashin man fetur duk lokacin da farashin danyen mai ya sauka.

Tasirin farashin danyen mai a duniya

A lokacin da Dangote ya ƙara farashin mai daga N899.50 zuwa N950, farashin gangar danyen mai a kasuwar duniya ya kai kusan $80.

Amma a halin yanzu, rahotanni sun nuna cewa farashin danyen mai ya sauka zuwa $75.67, wanda hakan ya taimaka wajen saukar da farashin man fetur a cikin gida Najeriya.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya samu: Dangote ya ƙara sauke farashin man fetur, ya faɗi sabon farashi

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Dangote Group, Anthony Chiejina, ya ce wannan matakin yana da alaƙa da sauyin da ya faru a kasuwar makamashi ta duniya.

Kiran Dangote ga ‘yan kasuwa

Anthony Chiejina ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su tabbatar da cewa an sauƙaƙa wa al’umma ta hanyar ragin farashin a matakin sayarwa.

Ya ce kamata ya yi ragin farashin ya bayyana a gidajen mai domin amfanar jama’ar Najeriya gaba ɗaya.

Sai dai bincike ya nuna cewa gidajen mai da dama a jihar Legas har yanzu na sayar da litar fetur a tsakanin N960 zuwa N990.

Martanin masu ruwa da tsaki

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƙungiyar Masu Gidajen Mai ta Ƙasa (IPMAN), Alhaji Olanrewaju Okanlawon, ya bayyana cewa samun saukin nuna fa’idar sauya tsarin dokokin kasuwancin mai.

Ya ce tsarin yana ba da damar daidaita farashin bisa ga halin kasuwa, wanda hakan ke sa kamfanoni kamar Dangote su rage farashi lokacin da yanayin kasuwa ya sauya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga kauye cikin dare sun yi wa mutane yankan rago

PETROAN ta ce farashin mai zai karye

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar 'yan kasuwar man fetur ta PETROAN ta ce nan gaba kadan farashin mai zai karye a Najeriya.

Kungiyar ta ce hakan zai tabbata ne bayan farfado da matatun Warri da Fatakwal da gwamnatin Najeriya ta yi a shekarar da ta wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel