"Allah Wadaran Naka Ya Lalace": An Yi Rubdugu kan Dan Arewa Mai Goyon bayan Tinubu
- Wani matashi daga jihar Sokoto ya shirya kaɗa ƙuri'arsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa
- Matashin mai suna Habibu Bello Mayana ya nuna cewa a shirye yake ya zaɓi shugaban ƙasan na Najeriya idan ya sake tsayawa takara
- Waɗannan kalaman na sa dai sun jawo ya sha suka wajen ƴan Najeriya waɗanda ba su ji daɗin goyon bayan da ya nunawa Tinubu ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Wani matashi mai suna Habibu Bello Mayana ya nuna goyon bayansa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Matashin ya bayyana cewa a shirye yake ya goyi bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 mai zuwa.

Asali: Twitter
Habibu Bello Mayana dai ya bayyana hakan ne a shafinsa na X mai suna @The_HBMayana.

Kara karanta wannan
"Baki ke yanka wuya," Atiku Abubakar ya jawo wa kansa abin magana kan 'batun N50m'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin ɗan jihar Sokoto ya nuna cewa ya gamsu da manufofi da ƙwarewar da shugaban ƙasan yake da ita.
Habibu Bello Mayana ya ba da tabbacin cewa a shirye yaje ya kaɗa ƙuri'arsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, idan Allah ya kaimu zaɓen 2027 da rai da lafiya.
Matashin ya rubuta cewa:
"Suna na Habibu Bello Mayana daga jihar Sokoto. Na shirya zaɓar Tinubu a 2027 Insha Allah."
Wane martani ƴan Najeriya suka yi masa?
Kalaman na matashin dai ba su yi wa wasu ƴan Najeriya daɗi ba, inda suka yi masa rubdugu.
Wasu daga cikin waɗanda suka yi masa martani dai, sun jefe shi da baƙaƙen maganganu kan goyon bayan da ya nunawa Shugaba Tinubu.
Ga kaɗan daga cikinsu:
@AMuhammad26483:
"Tir Allah ya wadaran naka ya lalace"
@jr___deen:
"Ka fara saka hular kwarai dai tukun 2027"
@Mohammednamadi2:
"Matsiyaci"
@ab_sanee:
"Wannan kuma ra'ayinka ne ɗan wahala"
@Auwalbalabakori:
"Rayuwarka ce, wa ya damu da hakan?"

Kara karanta wannan
"Za a tsige shi daga shugabancin APC?" An bayyana dalilin naɗa Ganduje a hukumar FAAN
@Gmatxai:
Toh kai kana tunanin za ka kai ko za mukai 2027? Rayuwar mu tana hannun ubangiji fa. Amma ko a nan kaɗai, Allah ya nuna maka cewa walahi talakawa basu tare da marasa tausayi. Insha Allahu da kai da duk wanda zai zabi T-pain sai kun sha kayi 2027."
Jigon APC ya caccaki ministan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Rivers, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya caccaki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Cif Eze ya soki Matawalle ne bayan ministan ya yi gargaɗi ga tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Chibuike Amaechi, kan sukar gwamnatin Bola Tinubu.
Jigon na APC ya buƙaci ƙaramin ministan da ya maida hankalin kan samar da tsaro maimaikon yi wa masu sukar gwamnati barazana.
Asali: Legit.ng